Shugaban Kwamitin Ilimi a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honorabul Mahmud Lawal (Bola Ige) ya bayyana cewa samar da jami’ar Musulunci ta farko a Jihar Kaduna alheri ne, domin za ta kara bunkasa ilimin addini Musulunci a fadin jihar baki daya.
Honarabul Bola Ige, wanda shi ne dan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Zariya, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron koli na kungiyar Fityanu da ya gudana a Jihar Kaduna.
- Sojoji Sun Kashe āYan Taāadda 185, Sun Kama 212, Sun Ceto Mutane 71 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
- Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Kasa
Shugaban kwamitin ilimin ya ce idan aka samar da jami’ar za ta taimaka wajen kara karfafa wa matasa sanin ilimin addinin Islama da na zamantakewa.
A kan hakan, ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayar da fili kyauta ga kungiyar Fityanu domin gina jami’ar da kuma jagorantar gininta.
Haka zalika, ya yaba wa gwamnan bisa irin gudummawar da yake bai wa harkar ilimi a Jihar Kaduna.