Farfesa Kingsley Moghalu, shugaban cibiyar nazarin jagoranci ta Afirka (ASG) da ke Kigali, Rwanda, ya ce Nijeriya na buƙatar sabon kundin tsarin mulki domin magance matsalolin siyasa, tattalin arziƙi, da rashin haɗin kai da ƙasar ke fama da su.
A cewarsa, yawancin shugabannin Nijeriya suna kauce wa tattaunawa kan samar da sabon kundin tsarin mulki ko sauye-sauyen da za su inganta rayuwar al’umma.
- Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura
- Sin Ta Yi Maraba Da Matsayin Da Najeriya Ta Samu Na Zama Abokiyar Huldar Gamayyar BRICS
Moghalu ya yi wannan jawabi ne a wata ganawa ta yanar gizo da aka gudanar kan jagoranci a Afirka, inda ya nuna damuwarsa kan halin da Nijeriya ke ciki.
Ya bayyana cewa dole ne a samar da daidaito tsakanin ƙabilu daban-daban domin samun zaman lafiya da ci gaba.
Ya ce, “Nijeriya ba za ta iya samun mafita ba har sai an koma teburin tattaunawa don tsara makoma mai kyau ga kowa.
“Sabon kundin tsarin mulki ne zai taimaka wajen kafa tsari mai ɗorewa da ci gaban tattalin arziƙi.”
Moghalu ya kuma jaddada cewa:
- Tattaunawa tsakanin shugabannin ƙabilu daban-daban na da matuƙar muhimmanci.
- Idan aka samu fahimtar juna, za a iya tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
- Shugabanni su daina kauce wa batutuwan da suka shafi ɗorewar ƙasar da inganta tsarin mulki.
Ya ƙara da cewa samar da kyakkyawan tsari zai taimaka wa Nijeriya ta tsayu kan ƙafafunta, ta inganta rayuwar al’umma, tare da samun tattalin arziƙi mai ƙarfi.
Moghalu ya yi kira ga shugabannin ƙasar da su mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa da samar da sabon kundin tsarin mulki wanda zai zama tushen zaman lafiya da ci gaba.