ALHAJI AHMED SULEIMAN mni shi ne Sarkin Misau da ke jihar Bauchi a hirarsa da wakilinmu KHALID IDRIS DOYA a makon jiya, bayan kammala bikin ba shi sandar mulki da Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya yi a matsayin sarkin masarautar Misau na 11 da aka yi a ranar Lahadi 13 ga watan Nuwamban 2022, ya bayyana cewar samar da hurumi ga sarakuna a cikin kundin tsarin mulkin kasa zai taimaka sosai wajen kyautata cigaban kasar nan ta fuskoki daban-daban.
Duk a cikin hirar, Sarkin ya ayyana wani buri da shirye-shirye ta cikin wata gidauniya da ya fito da ita, wanda ya ce ko waddan kawai Allah ya cika masa buri shi kan ya yi nasara kuma Alhamdullahi. Ga dai hirar:
Ran mai martaba ya dade, a lokacin bikin mika maka sanda, gwamnan Bauchi ya yi kira ga majalisar kasa da ta samar da wani hurumi wa Sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya yaya kuka ga wannan kiran?
Bismillahir Rahmanin Rahim. Muna godiya wa Allah madaukakin Sarki da ya ba mu sarari mu yi magana a kan wannan batun. Wannan batu ne mai muhimmanci, mecece ma’anar abin da nake nufi? Nan ana rantsar da Sarakuna a kan tsaren mulki amma ba su cikin shi din. Rantsuwar da aka ba mu muka yi ana cewa za mu bi umarnin tsarin mulki din Nijeriya, kundun mulkin kasa gabaki daya. Amma kuma ba mu ciki, don haka gaskiya akwai matsala a ciki. Kuma ina tabbatar maku cewa majalisar sarakuna ta kasa gabadaya sun kafa kwamiti har an je majalisar dattawa a kan wannan batun, muna dai rokon Allah ya sa a duba wannan al’amarin a kuma yi abin da ya dace. Ba za ka ce mutum kana son ya yi amfani ba, kuma ka ce ba ya da wani amfani ba duk a lokaci guda.
Wanne alfanu ake ganin wannan abin zai yi idan aka samu nasarar hakan?
Zai bai wa kowa damar ya yi amfani da mukamin da Allah ya ba shi domin a kawo zaman lafiya da cigaba a wannan kasar.
Wasu na ganin ko ba a yi wannan ba, ku Sarakuna ayyukan da kuke yi ma sun isheku na sasanta tsakanin jama’a, zamantakewa da bada shawarwari kusan wadannan ayyukan da kuke yi kamar ma baku ma da lokacin kanku?
Eh fadi ake yi, in ka samu tushe, ya zamana kana da tushen yin magana to ya fi alkairi. Wannan kam ai fada ake yi, za ka iya kiran talaka ya ce ai shi ba abin da aka masa kuma haka yake, tun da ba kada wani hurumi a cikin dokokin kasar nan.
Ya mai martaba zai kamanta rayuwarsa a baya da baya kan kujera da yanzu lokacin da yake sarki, kuma mene ne bambancin aikin sarauta da aikin gwamnati ganin cewa ka goge da dadewa a bangaren aikin gwamnati?
Alhamdullahi wannan abu ne wanda na yi bayaninsa a lokacin da Allah (Subhanahu Wata’ala) ya sa aka bani ‘Sanda’, banbancin shi ne yanzu al’ummar gaba daya suna kallonka ne kai kadai, da kana aikin gwamnati, kana karkashin wani ne sai abin da aka fada ko shawarar da za ka bayar, amma yanzu duk batun na wajenka, karshen maganar ta zo wajenka. Saboda haka wannan nauyin yana da muhimmanci yana da kuma ban tsoro, sai dai muna rokon Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar.
Mai martaba ya ce ba abin da yake so kamar ya ga cewa ya bar wani abu da koda bayan baya nan a tuna da shi, ko me kake nufi da wannan?
Babu wani da baya son tarihi, babu wanda zai so a manta da tarihinsa, in ka san amfanin tarihi to maganar da nake yi kenan. A tarihince a san ka yi abu kaza ka yi abu kaza, wannan ne zai sa ba za a taba mantawa da kai ba.
Yanzu akwai wasu ayyukan da Sarki yake son ya maida hankali wajen ganin ya cimma su a nan gaba a masarautar shi?
Babba ma kuwa, manya-manya ma kuwa. Amma alhamudllahi duk sun dunkula ne yanzu a kan wata gidauniya da muka saka ta raya kasar Misau wato ‘MEDEP’ a takaice, wannan gidauniyar tana da sassa har guda goma, kama daga wasa, kiwon lafiya, batun anfanin, ilimi da dai sauransu. In da a ce zan samu wannan gidauniyar ta zauna da gindinta ni Alhamdullahi na samu biyan bukatata.
Wannan gidauniyar za ta kawo sauye-sauyen da kake bukata kenan?
Insha Allahu, kuma ku taya mu da addu’a muma muna kai.
Ranka dade ko za ka mana karin haske kan wannan gidauniyar ta yaya za ta kasance kuma kai ne shugabanta, ganin cewa ka ce burinka na kanta?
Kwarai da gaske burina yana kai, amma ni zan ce kamar ni shugaba ne marar iko, amma akwai wadanda suke gudanar da ita, kuma kowani sashi yana da wanda yake shugantarsa. Misali, ilimi, sai muka dauko Farfesa Auwal Uba mukaddashin shugaban jami’ar Gadau sai yake kula da sha’anin da duk ya shafi ilimi, kama daga samun guraben karatu na yara da samun dukkanin agajin da suka shafi ilimi har taimakawa ga wadanda basu da hali wajen ganin an sama musu yadda za su yi karatun.
Sannan a bangaren kiwon lafiya, akwai Dakta Alkali wanda wata kila ka sanshi, ya matsayin Associate Professor ne yana asibitin kwararru da ke Bauchi to shi kuma yana kula da sashin lafiya. Haka duk sauran bangarorin muka yi domin ganin an samu nasara. In ka lura kafin a bani Sanda akwai gudunmawar da wannan gidauniyar ta bayar, ina tabbatar maka a kalla mutane 400 an duba lafiyarsu an basu magani a sanadin bada wannan sandar haka dabbobi da sauransu duk a sanadiyyar bada wannan sandar kawai. Don haka wannan gidauniyar tamu tana da fadi idan aka samu, ba wai muna yi mu cire aikin gwamnati ba ne, a’a muna yi ne don mu taimaka wa jama’anmu ne, mu taimaka a inda gwamnati ta dan kasa sai mu bada tamu gudunmawar.
Muna da masaniyar cewa duk a karkashin wannan gidauniyar an kaddamar da banki na al’umma, ta yaya za ta gudanar da aikinta za ta bayar da bashi da ruwa ne ko za ta bayar da bashi ba tare da ruwa ba kuma su waye za su mora masu karamin karfi?
Ina godiya da wannan tambayar taka, kuma ina son na jawo hankalin al’ummar karamar hukumar Misau da dukkanin wadanda suke da sha’awar kawo cigaba. Muhimmin abin da ake nufi shi ne wannan bankin ba na ruwa ba ne, shi ya sa aka kirashi ‘Ba riba a ciki- (Ba ruwa)’ za ka bada jarinka ko za ka je ka karbi bashi bisa abun da ka samu in riba ce ku ci ku raba da bankin tare in ma faduwa ce haka za ku raba tare. Shi ya sa aka ce wa bankin ‘Islamic Bank’ yana bin ka’idoji na addinin musulunci don haka babu zancen riba a ciki, kuma muna fatan yadda aka yi shi ya tabbata muna fatan ya zama alkairi ga kasar baki daya.
A zantawar da muka yi da al’ummar masarautar Misau kafin a baka sandar mulki, ka yi kokarin hada kan al’umma da wasu da suka samu sabani duk an sasantasu ko wane karin bayani za ka yi a kan wannan?
Ai abu mai sauki ne, tsintsiya daya bata shara. In ka hada kan jama’a kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa sai ka ga an samu cigaba shi ne dalili kuma shi ne makasudi domin kasar tamu ba girma take da shi ba, idan muka hada kai za mu fi samun nasara, wannan dalilin ne ya sa muka dauki wannan matakin na sasanta kowa da hada kan kowa.
Duk abun da ake nema shi ne a kau da talauci ya zama kowa na zaune lafiya, yana da abun da zai ci da abun da zai yi ba tare da tashin hankali ba.
A wajen baka sandar girma an ga al’umma masu dumbin yawa don za a iya cewa hakan ya shiga cikin tarihin masarautar nan, ka ji dadi kuwa a ranka?
Alhamdullahi ba wanda zai ga jama’a irin wannan ba zai yi godiya wa Allah madaukakin sarki ba. Muna godiya wa kowa da kowa, mun kuma ji dadi da Allah ya maida kowa gidasa lafiya.
Mun gode.