Bala Kukuru" />

Sampam Na Taka Kyakkyawar Rawa A Legas Kan Kasuwar Gwari – Kofa

Daya daga cikin jagororin bangarorin kasuwa yan-gwari a kasuwar Mile 12 intanashinal market Alhaji yusif dauda kofa ta karama hukuma bebeji dake jihar kano wanda shine shugaban bangaren gudanar da kasuwancin citta da tafarnuwa a kasuwar ta mile 12 intanashinal Market ya bayyana cewar bisaga jagorancin babbar kasuwar yan gwari a legas  Alhaji shehu usman sampam yana taka rawar gani tareda gudanar da kyakkyawan jagoranci  al-umma dana kasuwar bakidaya.

Alhaji Yusuf dauda kofa yayi wan nan tsokacin ne a office dinsa dake kasuwar ya yan gwari a legas a lokacin da yake zantawa da wadansu wakilan kafofin yada labrai na kasa kuma yake hurta ra’ayinsa a gameda cigaban da yake ganin kasuwar ta karasamu a daidai wannan lokacin, kofa ya cigaba da cewar babu shakka bisaga jagoranci  shugaban kasuwar Alhaji shehu usman sampam kasuwar ta yan gwari  ahalin  yanzu ta kara samun tasiri tareda martaba ga al-ummar Nijereya da sauran jama’ar da suke kawo kayan gwari daga wandansu kasashen ketare wandanda suke makwabtaka da nijeriya domin sayar ma al-ummar tareda gudanar da harkokin kasuwancin gwari a duk fadin kasa nan ya kara da cewa akan haka yake kara jinjinawa dattawan kasuwar ta mile12 intanashinal maket da sauran shuwagabanin bangarorin kasuwar da sukayi zurfin tunani na kawo Alhaji shehu sampam tareda zabarsa a matsayin wanda zai cigaba da jagorancin kasuwar.

Daga nan zuwa wani lokaci ya cigaba da cewar wannan al-amari ya farantawa dukkan masu gudanar da sana’ar gawri rayuwa bisaga bunkasa harkokin kasuwancin gwari da yakeyi awan nan kasuwa da nijeriya baki daya

Sannan kuma ya ummurci shuwagabannin bangororin kasuwar da ban da ban  da sucigaba da bayar da tasu gudunmuwar tareda ba shugaban  kasuwar Alhaji shehu usman sampam hadin kai da goyan baya a wajen cigaba da gudanar da aiyukan cigaban kasuwar ta mile 12 intanashinal maket domin kwalliya ta biya kudin sabulu, a kokarinsa na ciyar da kasuwar yan gawri gaba a cewarsa kuma da ikon ubangiji  suma shuwagabannin bangarorin kasuwar za sucigaba da yin koyi da irin wadan nan   aiyukan na cigaban  kasuwar yan gawri dake anan cikin garin legas.

Sannan yakara ummurta abokan aikinsa na bangaren kasuwacin citta da tafarnuwa dasu hada kawunan junansu a wajen cigaba  da bunkasa harkokin kasuwacin citta da tafarnuwa a wannan babbar kasuwa mai albrakan dake cikin gain legas da Nijeriya bakidaya sannan yakara da cewa akan haka yake kara isar da sakon godiyarsa ga dattawan kasuwar a karkashin jagorancin shugaban kungiyar dattawan Alhaji isah muhammed da Alhaji haruna muhammed tamarke  da Alhaji habu paki da Alhaji abdulwahab tsoho babangida da Alhaji abdullahi burama da tsohon sakataran kasuwar Alhaji wada yaro da sauran makaman tansu ya cigaba da cewar wadan nan sune dattawan kasuwar ta yan gwari injishi wanda da sanya hanunsu ne kasuwar take samun cigaba ahalin yanzun ya kara da cewar hakama uwa kuma uba a kasuwar ta mile 12 intanashinal Market tsohon sifikar majarlisar dokokin jihar kano Hon, Alhaji Kabiru Alasan rurum kuma Dan Majalisar wakilai ahalin yanzun mai wakiltar kananan hukumomin kibiya da rano a zuren majalisar wakilai dake abuja wanda acewarsa shima yabada tasa gudunmawa kwarai da gaske a wajan hada kawunan al-umma kasuwar ta mile 12 domin cigaba da samu n zaman lafiya a kowanne lokaci injishi da fatan Allah ya saka masu da alheri ya kuma cigaba da yimusu jagorancin al-umma acikin adalaci a wajan al-amuransu na yau da kullum.

Exit mobile version