Darakta Janar na Hukumar da ke kula da hannayen jari ta kasa (SEC), Dakta Emomotimi Agama, ya jaddada cewa, samun nasarar da Nijeriya ta yin a Naira tiriliyan daya a tattalin azrkin kasa, ba wai kawai ta samu haka ba ne, amma wani abu ne, da ya zama babbar nasara da kuma jajircewar kasar.
Dakta Agama ya sanar da haka ne, a jawabin da ya yi a wajen taron gabatar a taron Hukumar na 2024.
- Sin Za Ta Ajiye Hatsi Kimanin Tan Miliyan 420
- Zargin China Da Bautar Da Leburori a Gonar Tumatir a Xinjiang: Mene Ne Gaskiyar Lamarin?
Taken kasidar da ya gabatar a wajen taron “ Gudunmawar Da Kasuwar Zuba Hannayen Jari Ke Takawa Wajen Bunkasa Tattalin Azikin Dala Tiriliyan Daya Na Nijeriya.”
Agama, wanda John Briggs Shugaban Sashe na Hukumar da ke shiyyar jihar Legas ya wakilce shi, inda ya sanar da cewa, kasuwar ta ci gaba da kasancewa, a matsayin wata jigo da ke kara habaka tattalin arzikin kasar, ta hanyar kara tura kudade na masu aiya da suke bukatar kudaden domin yin amfani da su.
A cewarsa, a daukacin fadin duniya kasashe sun samu bunkasar tattalin arzikinsu ne, ta hanyar ayyukan masana’antu, fasahar kere-kere da sauransu, musamman duba da yadda suka dogara a kan kasuwannin su na zuba hannun yin tare da kuma zuba kudaden yadda ya kamata.
Ya ci gaba da cewa, Nijeriya na da damarmaki da dama, inda ya yi nuni da cewa, bisa samar da tsrare-tsaren da suka kamata, da karfafa guiwar masu son zuba hannun jari a cikin tattalin arzikin kasar, kasuwar za ta kara kasancewa tamkar wata ginshiki wajen kara bunkasa tattalin arzikin Niijeriya
Agama ya kara da cewa, jimlar kudin da kasuwar ta samar yanzu, ya kai matsayin Naira tiriliyan 60, inda ya bayyana cewa, wannan nasarar ta nuna yadda kamfanoni masu zaman kansu suke taka gagaruwar rawa a fannin kara habaka tattalin arzikin kasar.
Ya bayyana cewa, kasuwar ta kuma kasance wata kashin bayan kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Shi kuwa a na sa bangaren a cikin wata kasida da ya gabatar a wajen taron mai taken “ Dogaro a Kan Fasahar Kimiyyar Zamani Don Janyo Matasa Shiga Kasuwar Hada-Hadar Musayar Kudi” Dakta Akeem Oyewale, Babban Shugaba a Kamfanin Zuba Hannun Jari ya sanar da cewa, matasa na da gudunmawar da za su bayar a cikin kasuwar.