Ɗaya daga cikin matasan jarumai a Masana’antar Kannywood, wanda a yanzu haka ludayinsu yake kan dawo, Baba Sadiƙ ko kuma Auwal Labarina, ya bayyana cewa; samun kuɗi ya fi samun daukaka matuƙar wahala a masana’antarsu ta shirya fina-finan Hausa.
Sadiƙ, a wata hira da ya yi da jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’, ya bayyana cewa; akwai lokacin da ya tafi karɓo lambar yabo ta gwarzon jarumi mai tasowa, amma a kafa ya dawo gida riƙe da lambar yabon, sakamakon rashin abin hawa a wancan lokaci.
“A lokacin da na fito a cikin shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in, na samu kyautar lambar yabo ta gwarzon jarumi mai tasowa, wanda na je na karɓa, amma bayan na fito daga wajen taron, sakamakon rashin abin hawa; a ƙarshe da ƙafa na taka har zuwa gidanmu”, in ji Sadiƙ.
- Shirin Bunƙasa Ilmi A Kano: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida Ta Tura Dalibai 1001 Karatu Kasashen Waje
- Kasar Sin Da Namibia Sun Sha Alwashin Daukaka Hadin Gwiwarsu Na Cin Moriyar Juna
Ya ƙara da cewa, yanzu ya fi mayar da hankali a kan abubuwan da yake ɗorawa a shafukansa na sada zumunta, musamman ‘Facebook’, da ake biyan sa maƙudan kudaɗe.
Sadiƙ ya ci gaba da cewa, samun daukaka babu kuɗi matsala ce babba, domin kuwa idan ka samu daukaka, ba kowace irin sana’a za ka iya yi ba; domin duk abin da ka yi, idanun mutane yana kanka, ni a lokacin da nake harkokina kafin na samu wannan daukaka, daukar hoto na ke yi; sannan kuma ina tuƙa Adaidaita Sahu, amma bayan na samu daukaka an fara sani na, sai na ji ba zan iya ci gaba da wadannan sana’o’i ba, duk da cewa kuma ba ni da kuɗi, amma sai naji a raina cewa; ba zan iya ci gaba da yin su ba, kamar yadda ya bayyana.
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri.
da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba ne ya jawo haka illa tsarin biyan kuɗi (Monetization) da kamfanin ‘Facebook’ ya fito da shi, domin yanzu na zage damtse ina neman kuɗi, ba tare da wasa ba, kafin yanzu ina ɗora bidiyon shawarwarin da za su taimaki al’ummarmu, amma kuma su mutanen da ke kallo sai na ga kamar ba su da ra’ayin ire-iren wadannan abubuwa da nake ɗorawa a shafin nawa.
Bayan daukar tsawon lokaci ina yin wadannan bidiyoyi na shawarwari, sai na yanke shawarar yin watsi da shi na koma ɗora bidiyoyina tare da abokan aikina ƴan fim, musamman idan muka haɗu a lokeshan na daukar fim, daga wannan lokaci ne sai na ga yawan ‘likes’ da ‘comments’ ɗin da mutane suke yi a shafi nawa ya ƙaru sosai, sannan adadin mutanen da ke ziyartar shafin shi ma ya ƙaru, sai kuma ga shi ina samun dalar Amurka fiye da 300 a duk lokacin da na ɗora ire-iren wadannan bidiyoyi nawa a shafin, sai kawai na ci gaba da yin hakan.
daga wancan lokacin da na fara ɗora bidiyoyi nawa tare da jarumai mata ƴan fim da sauran sanannun mata, na kan samu aƙalla Naira Miliyan biyar zuwa 10 a duk wata daga abin da ‘Facebook’ ke biya na, don haka yanzu na gane cewa; talauci ne matsalata a lokacin baya, kuma Alhamdulillahi yanzu na fara samun sauƙin wannan matsala a halin yanzu da hanyoyin samu suka ƙara buɗe min, in ji shi.
daga ƙarshe, Baba Sadiƙ ya ce; kamata ya yi a ce matasa su mayar da hankali wajen abubuwan da za su taimake su a rayuwarsu, ba su tsaya suna faɗin aibin wani ko yaba burgewar wani ba, yanzu matasa da dama su kan ɓata lokacin su wajen aibata wani idan ya yi kuskure, ko kuma yabon wanda bai ma san suna yi ba, ba komai ne ke jawo irin haka ba; illa rashin aiki da mafi yawancin matasa ke fama da shi, a maimakon ka tsaya cewa; Rarara ya sai sabuwar mota ko kuma Hadiza Gabon ta yi ‘Slimming’ gara ka je ka nemi abin da za ka rufa wa kanka asiri, kamar yadda ya shawarci matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp