Kamar yanda ake shigar da kayayyaki daga kasashen waje haka ma ana iya fitar da kayakin da ake noma ko kuma ake samu daga kasar Nijeriya zuwa wasu kasashen ketare.
Sana’a ce mai matukar riba yayin da aka Fara ta.
- An Bude Dandalin Hadin Gwiwa Da Raya Kirkire-kirkire Na Sin Da Afirka
- Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Barkewar Cutar Diptheria A Abuja
Farkon abin da ya kamata mai yin wannan sana’a ya samu idan zai fara wannan sana’a shi ne Tsarin kasuwanci da kuma fadada bincike. Idan kaki bincike, to za ka fadi kwata-kwata saboda fitar da kaya ya na bukatar muhimman bayanai kuma idan ba ka da Tsarin kasuwanci mai kyau, za ka fadi maimakon riba da ya kamata ka samu.
Wane Irin Kaya Za Ka Iya Fitarwa?
Kayayyakin da za Ka iya sayar da su waje na da matukar yawa don sun hada da kayayyakin da muke kerawa a kasar da muke ci kamar su daddawa, garin albo, Garin Amala da sauran su.
Kafin ka fara ya kamata ka san wadanan abubuwan.
- Wane irin kaya ne kake sha’awar fitarwa?
- A ina ake samun wadannan kayan, wa ke son saya, ka san ko su waye kwastomomin ka?
3.kuma me suke son saya? 4. Nawa kake bukata yayin fara wannan sana’ar?
- Nawa kake da shi? 6. Shin yana da riba? 7. Mene ne kasuwancinka yake samar maka din ka? 8. Ta ya kake da niyyar hada girman jarin ka? 9. Mene ne dajarar musayar kuDi a yanzu? 10. Wane lokaci ya kamata ya kai da za ka samu kudinka?
- Kuma yaushe za ka samu kayan? saboda wasu kayan ba a samun su sai lokaci lokaci.
Ya kamata ka san yadda za ka yi sufuri ko jigilar kayan, shi ma yana da matukar muhimmanci ka sani musamman idan masu nauyi ne ko a’a.
Sai Ka Yi Registar Kamfaninka Da Hukuma
Wannan shima yana da amfani a wannan sana’ar, zai sa ka zama abin dogara da kuma kara maka yarda. To bayan ka gama yin tunani, lokaci ya yi da za ka yi rajistar sunan sana’arka da Hukuma kula da kasuwanci ta kasa ‘Corporate affairs commission’.
rajistar na da matukar muhimmanci idan za ka nema kuma ka samu lasisin daga ‘National edport promotion council,’ (NEPC) da kuma takardar shaida ‘Certificate’.
Sana’arka dole ne a yi rajista ta da Limited Liability Company (kamfani mai iyaka), cooperatibe society (al’ummar hadin kai), ko gwamnati ko kuma ba na gwamnati ba.
Bayan ka yi rajistar sana’arka da kuma sunanta, samun lasisi na NEPC shi ne na gaba. kuma ya kamata ka samu wadannan abubuwan.
- Takardun da ake bukata don samun lasisi na NEPC, kana da bukatar wannan takardu ne dangane da kuma wace irin sana’a kake yi wa registan NEPC.
idan limited liability company ne wato kamfani me iyaka za ka bukaci wadannan abubuwan:
- Certificate of incorporation (takardar shaidar hadawa), certified true copy of memorandum and articles of association,certified true copy na cac 1.1 section c (bayanan directoci) wanda da ake kira form co7 ko kuma cac 7, na cooperatibe society (al’ummar hadin kai) bukatar rajista ta daban yake za ka iya yin rajista ne ta intanet ko kuma ka je offishin NEPC na jiharku, idan ka je za ka :
Sayi form na ragista Naira 1000, za ka biya 13,500 na ragista da processing fee.
Sai ka kai musu form din da ka cike na rajista a NEPC tare da wadannan takardun
Photocopy na certificate of incorporation na kamfani.
Yadda za ka nema kwastomomi
Za ka iya samun kwastomomi ta hanyoyi da dama wanda ya hada da abokan arziki da kuma yan uwa masu zama a kasashen ketare ta hanyar tura musu idan wani ya gani ya ji dadin amfani da shi za ka ga ana ta neman ka.