Sanata A Karkashin PDP Ya Bayyana Shakkun Yin Zabe A 2023

Abaribe

Daga Yusuf Shu’aibu,

Wani sanatan a karkashin jam’iyyar PDP Abaribe ya bayyana dalilin da yake shakkun gudanar da babban zaben shekarar 2023.

Sanata Abaribe ya bayyana cewa, dole ne gwamnatin tarayyar Nijeriya ta gyara matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan a halin yanzu. Dan majalisar karkashin tutan jam’iyyar PDP ya kara da cewa, idan matsalar tsaro ta ci gaba a haka, ba lallai ba ne a iya gudanar da babban zaben da ke tafe a shekarar 2023 ba. Abaribe ya caccaki gwamnatin APC da Buhari ke jagoranta, yana mai cewa ta kasa magance matsalar tsaron da ke addabar kasar nan.

Sanata Enyinnaya Abaribe shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya ce ba za a iya gudanar da babban zaben shekarar 2023 ba idan har ba a magance matsalar tsaro a cikin kasar nan yadda ya kamata ba. Ababribe wanda ke wakiltar Abiya ta Kudu a majalisar dokokin tarayyar ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Daily Sun ta wallafa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu. Ya ce, kusan dukkan sassan kasar nan ba su da kwanciyar hankali musamman ma a yankin Kudu wanda a baya ya kasance mai kwanciyar hankali.

Sanatan ya ce,”Abu mafi mahimmanci a yau shi ne, ba mu san ko babban zaben shekarar 2023 zai yiwu ba, domin mutane suna ta magana.

“Akwai tsoron ta’addanci. Babbar matsalar yanzu ita ce rashin tsaro. Ba ma so mu yi watsi da abin da zai iya karya kasar kuma mu mai da hankali kan batutuwa na lokaci-lokaci kamar zabukan da watakila ba za a yi ba.”

Ababribe ya koka kan yadda Kudu-Maso- Gabashin kasar nan da ke da tsaro a baya yake fuskantar karuwar ta’addanci a halin yanzu. Sanatan na PDP ya zargi gwamnatin da Buhari ke jagoranta da rashin cika alkawarinta na magance rashin tsaro a cikin kasar nan.

Ya ce, “shekaru shida a jere ya tabarbare. Akwai bukatar mu fada musu cewa su yi kokari su gyara matsalar,” in ji shi.

Exit mobile version