Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya ƙaddamar da rabon kayan Tallafi ga mazabun Kebbi ta tsakiya a kananan hukumomi takwas da yake wakilta a majalisar dattijai.
Kananan hukumomin da zasu cigajiyar sun ha da Birnin Kebbi, Kalgo, Bunza, Jega, Aliero, Gwandu, Maiyama da Koko Besse. Inda aka raba kayayyakin kamar haka: Keke napep (tricycles) 150, babura 114, Deep Firijen 204, fridge 302, Injimin nika 740, keken dinki 800.
- Kotu Ta Daure Wasu Mutum Biyu Da Suka Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 14 Fyade A Birnin Kebbi
- ‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Da Ake Zargi Da Satar Mota A Kebbi
Sauran sun ha da na injunan ban ruwa guda 500 sai buhuhuwan Taki gudu 13,400 Waɗanda mata da Maza na dukkan Waɗanda mazabun kananan hukumomin Takwas a jihar ne za su cigajiyar kayan Sanatan.
Haka kuma an gudanar da rabon kayan ne a garin Aliero, a karamar hukumar Aliero a cikin jihar, rabon kayan yana cikin ayyukan sanata Muhammadu Adamu Aliero da yake gudanar wa a bangaren tallafi da karfafawa rayuwar jama’ar da ya ke wakilta.
A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp