Sanata Samuel Anyanwu ya lashe zaben fitar da gwani na takarar kujerar gwamnan Jihar Imo a karkashin jam’iyyar PDP da kuri’u 802.
Idan za a tuna dai, mako uku da suka gabata, babban abokin karawarsa, tsohon gwamnan Jihar Chief Emeka Ihedioha, ya janye daga neman tikitin na jam’iyyar ta PDP.
Wakilan jam’iyyar 802 da suka fito daga kananan hukumomi 27 ne suka zabi Sanata Anyanwu domin ya rike tuta wa jam’iyyar a zaben gwamnan, yayin da sauran ‘yan takarar suka samu kuri’u 23 yayin da kuri’u 28 kuma suka kasance marasa kyau.
Shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin a jihar Imo, Rt. Hon. Kenneth Okon, da sakataren kwamitin, Olalekan Rotimi, su ne suka ayyana Sanata Anyanwu a matsayin wanda ya lashe zaben tare da samun tabbacin shugaban jam’iyyar a jihar, Injiniya Charles Ugwu.
A jawabinsa na godiya, Sanata Samuel Anyanwu ya nuna matukar godiyarsa bisa yadda wakilan jam’iyyar (Delegates) suka fito suka masa ruwan kuri’u, ya bukaci jama’an jihar da su fito su zabi PDP a yayin zaben da ke tafe.
Ya yi alkawarin cewa zai yi aiki da dukkanin wadanda za su taimaka masa wajen samun nasara.”