Khalid Idris Doya" />

Sanata Babayo Gamawa Ya Rasu, 53

Allah ya yi rasuwa wa Sanata Babayo Garba Gamawa, wanda tsohon Sanata ne kuma Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, kana tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Marigayin dai fitattaccen dan siyasa ne a jihar Bauchi wanda ya ke da tasiri a siyasar jihar ta Bauchi. Ya rasu ne jiya Juma’a a jihar Bauchi a sakamakon rashin lafiyar da ta addabeshi.

Mai magana da yawun marigayin, Isah Garba Gadau ya tabbatar da rasuwar na Gamawa a hirarsa ta wayar tarho da ‘yan jarida, “Ya yi korafin cewar cikinsa na ciwo sai aka daukeshi zuwa asibitin koyarwa ta ABUTH da ke Bauchi domin kulawar likitoci,” A cewar shi.

Wakilinmu ya shaida cewar marigayi Gamawa yana daya daga cikin manyan ‘yan siyasa a jihar Bauchi wanda ya yi takarar gwamnan a jihar Bauchi bai ci ba, amma ya rike mukaman mataimakin gwamna, dan majalisar tarayya kana ya

rike shugaban masu rijaye a majalisar dokokin jihar Bauchi kuma zama

Kakakin majalisar jihar Bauchi, a mukamin da ya rike a baya-bayan nan shine mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

An haifi marigayi Sanaga Gamawa ne dai a ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar 1966, ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.

A gefe guda marigayin dan kasuwa ne fitattaccen dan siyasa a arewacin Nijeriya, ya zama sanata ne a shekarar 2011 wanda ya wakilci mazabar Bauchi ta Arewa a majalisar dattawa ta kasa ta bakwai, kusa ne kuma fitacce a jam’iyyar PDP.   

Gamawa ya dale kujerar mataimakin gwamnan jihar Bauchi kuma tsohon Kakakin majalisar jihar, ya zama mataimakin gwamnan Bauchi ne a lokacin da aka tunbuke Alhaji Muhammad Garba Gadi daga kan kujerar.

Exit mobile version