Daga Jamil Gulma Birnin,
A cikin shirin sa na inganta lafiyar al’umma a mazabarsa ta gundumar Kebbi ta Arewa Sanata Dokta Yahaya Abdullahi shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya raba kayan aikin asibiti na milliyoyin nairori a kananan asibitoci.
Alhaji Abubakar Musa Argungu wanda shi ne ya wakilci Sanata Dokta Yahaya Abdullahi a wajen bukin rabon kayan ya bayyana samun wakilci irin na Sanata shi ne burin kowace al’umma saboda ba kansa ya je azurtawa ko dimama kujera ya je yi a majalisar dattawa ba ya je ne don wakiltar al’ummarsa kuma ba shakka ya isarda wakilci saboda tun tarihin siyasa a iya sanin sa ba a taba samun irin wannan wakilcin ba.
Ya yi kira ga jami’an da aka hannantawa wadannan kayan da su ji tsoron Allah su yi amfani da su yadda ya kamata kada su bi wadansu hanyoyi da bai kamata ba saboda idan ana yin haka da kayan ba su iso hannunsu ba.
Kayan dai sun hada da gadaje da katifu, tebura da kujeri, kayan awo dabam-daban, injinan wuta, Firjin, Babura, kabot-kabot, kujerin ofis, bokitai da kayan tsaftace asibiti da dai sauransu.
Taron dai ya sami halartar yansiyasa, ma’aikatan hukumar lafiya a matakin farko na kasa da jiha, shugabannin sashen lafiya daga kananan hukumomin Argungu, Augie Arewa, Dandi, Bagudo da Suru.