Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Dr Yahaya Abubakar Abdullahi ya ja kunnen matasa da su kasance jekadu nagari.
Wannan bayanin ya fito daga bakin mataimaki kan al’amurra na musamman Alhaji Ayuba Umar a garin Birnin Kebbi jiya Talata lokacin da tawagar wakilan Sanatan suka ziyarci matasa masu rubuta jarabawar shiga ayukan shige da fice, kashe gobara, gidan gyara halinka da kuma aikin tsaro na farinkaya da suka fito daga gundumar mazabar Kebbi ta Arewa da suka kumshi kananan hukumomin Argungu, Augie, Arewa, Dandi, Suru da kuma Bagudo.
Alhaji Ayuba Umar ya ce maigirma Sanata yana yi musu fatar alheri da kuma ba su kwarin gwiwa wajen shiga gwagwarmayar neman kowane irin aiki idan aka nemi matasa su shiga.
Ya cigaba da cewa kamar yadda aka san yayan jihar Kebbi da jarunta a duk inda suka shiga a nan ma yana fatar ba za a bar su a haha ba kuma don Allah su zamo jekadu nagari musamman a wannan lokacin da kasar nan ke fama da matsalar tsaro.
Usman Lena daga karamar hukumar mulki ta Arewa a madadin sauran matasan ya yabawa Sanata Dr Yahaya Abubakar Abdullahi bisa a kulawarsa ga mutanen da ya ke wakilta wanda suna sane da irin kokarin da ya ke yi a duk lokacin da irin wannan ta taso, an yi daukar sojoji ya turo wakilansa, an yi daukar dalibai a makarantun gaba da sakandare musamman jami’o’i bayan ya raba fom-fom na sharefage ga matasa har wa yau ya turo wakilansa don bin dugin samun gurabun karatu ga daliban, ya aiko an koyawa matasa maza da maza sana’o’i don su dogara da kawunansu da dai sauran abubuwa da yawa saboda haka muna yi masa fatar alheri.
Ya yi kira ga yansiyasa musamman zababbu da su yi koyi da shi kada su ba su fafa gora sai ranar tafiya.