Abba Ibrahim Wada" />

Sanches Zai Koma Atletico Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta tuntubi dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Aledis Sanches akan ko zai koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa bayan da kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer ya ce da dan wasan baya bukatarsa a kakar wasa mai zuwa.

Sanches, mai shekara 30 a duniya ya koma Manchester United ne daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a watan Janairun shekara ta 2018 inda kuma ya zura kwallaye biyar cikin wasanni 45 din daya bugawa United din.

Sai dai tun bayan da Solkjaer ya koma kungiyar a amtsayin mai koyarwa aka fara danganta dan wasan da barin United inda kungiyoyin Juventus da Inter Milan duka daga kasar Italiya suka nuna sha’awarsu ta daukar dan wasan dan asalin kasar Chile.

Har ila yau wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta tuntubi dan wasan ko zai sake komawa gasar laliga domin ya buga musu wasa bayan da tun farko ya bugawa Barcelona wasa amma sai dai idan zai rage albashinsa.

Sanches wanda ya buga wasa a karkashin kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone a kungiyar Riber Plate a shekara ta 2007 yanada ragowar kwantirangin shekara uku a United kuma yana daukar albashin fan dubu dari biyar a sati daya.

Exit mobile version