Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Sanin Yadda Ake Mulki Ne Yasa Turawa Kafin Su Koma Suka Mika Hannun Arewa – Hamza  

by Muhammad
January 22, 2021
in LABARAI
3 min read
Mulki
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Hamza Sani shi sakatare ne na kungiyar masu sayar da Kaji ta jihar Nasarawa bugi da kari kuma shi mataimaki ne na musamman ga Alhaji Aliyu Musa Turaki Tafidan Gurku, a hirar da ya yi da manema labarai wanda ciki har da Idris Aliyu Daudawa wakilin jaridar LEADERSHIP Ayau ya bayyana yadda wadansu al’amuran da suke ci masa tuwo a kwarya, musamman ma idan aka yi la’akari akan yadda ita Arewar take a shekarun baya da kuma yanzu, sai kuma hango ita ma kasar Nijeriyar da ya yi baki daya, sai ayi karatu lafiya.

samndaads

 

Hamza ya fara bayyana cewar abinda zai ce shi ne ‘Yan Arewa sun iya mulki shugabanci da kuma mulki saboda kuwa idan aka duba tarihin Arewa bayan mulkin mallaka, saboda iya mulkin na ‘yan Arewa kamar dai yadda su Turawan suka lura basu bar kasar a hannu kowa ba sai hannun shugabannin al’ummar na ‘yan Arewa. Bugu da kari kuma nau’in na shugabannin na Arewa sune wadanda basu nuna wani bambancin addini, siyasa, ko kuma kabilanci. Saidai kuma da aka samu tuntube ne wasu al’amuran suka canza daga yadda aka san su can baya, amma kuma wani al’amari da shi wannan na daban ne har yanzu wadanda suke rika da madabun iko a Nijeriya ‘yan Arewa sun eke kan gaba da kowa.

Da aka tambaye shi ko mi yasa shugabannin siyasar Arewa na yanzu basu cika yi koyi da abubuwan da su marigayi Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa da kuma Abubakar Tafawa Balewa wadanda suka kafa ginshikin cigaban Nijeriya, sai ya bada amsar cewar.Ya ce kamar dai yadda aka tambaye shi cewar yanzu abubuwa sun riga sun sauya, kamar irin wadanda Kakannin mu da suka kafa ita kasar suka tafi suka barta .An kuma samu hakan ne saboda tabarbarewar al’amarin tattalin arziki da kuma yadda al’amarin cin hanci da rashawa ya shi go kasa. Wannan ne abinda ya bata yadda ake tafiyar da shi mulkin, sai dai wani abu kuma idan aka yi la’akari da yadda kasar take tafiya duk da hakan mutanen Arewa sun taka rawar data kamata.

 

Ya kuma kara jaddada cewar su shugabannin siyasar Arewa idan dai ba mantawa aka yi ba sun taka rawar gani, wajen kafa wata turba wadda idan muka kalla za muyi farin ciki, na cewar Kakannin mu basu bar mana abinda zai sa a rika yi mana a gaba ba.

 

Idan kuma aka duba ta bangaren yadda shi sashen na Arewa shi ne wanda ya fi samar da shugabannin kasa masu yawa, tiun daga lokacin da aka samu mulki daga Turawan mulkin mallaka, amma kuma al’ummar wancan sashen ne suka fi kowa a cikin kasar shiga mawuyacin kuncin rayuwa ta talauci fiye da su sauran sassan wadanda ‘yan wadancan sashen basu shugabanci kasar ba kamar yadda na Arewa suka yi. Wannan tambayar kuma shi cewa ya yi:Gaskiya a duk lokacin da aka ce shugabannin ku suka samu yakar jahilci wannan ba karamin aiki bane suka yi saboda kuwa, saboda kuwa jahilci shi kadai yana samar da talauci, saboda kuskuren da muka samu shi ne shi al’amarin ya dade yana bin mu sau da kafa, bugu da kari kuma su irin wadannan matsaloloin da aka samu cikin kasa sune suka taimaka ta bangaren tsaro.Babu abinda ya haifar da su sai jahilci, Ba yadda za ayi in banda akwai jahilci cikin rayuwar dan Adam ace da wani makami da wani abinda bai taka kara ya karya ba, ace ma ka je kashe mutum dan’uwanka mu watakila ma yankin ku daya ko jiharku ne kawai akan dan abinda ba zai iya kashe maka kishirwar data dame kaba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jihar Kano Ta Sake Fadada Dokar Yaki Da Korona Zuwa Kulob-kulob

Next Post

Matar Sheikh EL-Zakzaky Ta Kamu Da Korona, In Ji Danta

RelatedPosts

miyagun kwayoyi

Masu Garkuwa Da Mutane Muggan Kwayoyi Suke Bukata Matsayin Kudin Fansa – NDLEA

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Shugaba kuma babban jami’i na Hukumar...

UNICEF Ta Yi Tir Da Sace ‘Yan Matan Makaranta A Jihar Zamfara

UNICEF Ta Yi Tir Da Sace ‘Yan Matan Makaranta A Jihar Zamfara

by Sulaiman Ibrahim
2 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Hukumar UNICEF ta bayyana damuwa tare...

Kwalejin Kimiyyar Lafiya Ta Aminu Dabo Ta Yaye Dalibai

Kwalejin Kimiyyar Lafiya Ta Aminu Dabo Ta Yaye Dalibai

by Sulaiman Ibrahim
2 hours ago
0

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kwalejin kimmiyar lafiya da fasaha ta...

Next Post
Zakzaky

Matar Sheikh EL-Zakzaky Ta Kamu Da Korona, In Ji Danta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version