Shehu Dikwa na jihar Borno, Alhaji Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, ya rasu.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar da mutuwar a garin Biu, jim kadan bayan gabatar da ma’aikatan ofis ga mai martaba Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar Mustapha da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi a ranar Asabar.
Za ayi jana’izar a garin Maiduguri ranar Asabar da karfe 5 na yamma.