Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya jinjinawa shugaba Bola Ahmad Tinubu kan bada aikin hanyar da ta taso daga marabar Kankara zuwa cikin birnin Katsina.
Sarkin ya yi wannan jinjina ne a lokacin da ‘yan kwangilar suka kawo masa ziyarar ban girma da sanar da shi wannan gagarumin aiki wanda suka ce zai lakume biliyoyin nairori.
- Jihar Kano Na Shirin Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomi – Gwamna Abba
- Abokan Kasuwancinmu Na Zuwa Akai-akai Don Neman Kayayyakin Da Mu Ke Tacewa- Dangote
Idan za a iya tunawa, hanyar an sake inganta ta ne tun a shekarar 1997 wanda yanzu haka ta koma wani sansani na haddasa haɗura da ɗaukar rayuka.
Mai Martaba ya nuna mahimmancin sake gina wannan hanya inda ya ce, lallai zata taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da zirga-zirga a wannan yanki musamman ga manoma da ‘yan kasuwa da sauran jama’a.
Haka kuma Sarkin ya koka game da hanyar da ta taso daga Kano zuwa Katsina, wacce tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya bada aikin ta, yau shekara bakwai da bada aikinta amma har yanzu ko rabi ba a yi ba.
Don haka, Sarkin ya yi kira ga Gwamnatin Shugaba Tinubu da ta kara sanya ido kan hanyar Kano zuwa Katsina domin ganin an kammalata.