Basarake Mai daraja ta daya a Zamfara, Sarkin Maru Abubakar Mai Gari, ya tsallake rijiya da baya yayin kai masa hari da ‘yan bindiga sukai masa a gidansa da ke hedikwatar Karamar Hukumar Maru, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu a fadar a jiya Alhamis.
‘Yan bindigar tun a ranar Laraba da ta gabata ne suka kai wa Sarkin harin har zuwa jiya Alhamis, inda suka ci karo da tawagarsa suka bude musu wuta.
- Kamata Ya Yi Gwamnatin Amurka Ta Yi La’Akari Da Dalilan Karbuwar Gwamnan Jihar California A Kasar Sin
- Tsohon Firaministan kasar Sin Li Keqiang Ya Rasu
Ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa, “’yan bindigar sun mamaye fadar Sarkin ne inda suka bude wuta ba kakkautawa a kokarinsu na kashe Sarkin, Allah ya tseratar da shi.
Amma nan take ‘yan bindigar suka kashe mutane hudu daga cikin akwai dogarinsa, suka jikkata wasu da dama kuma sun lalata motocin sarkin.
Haka kazalika yanzu haka gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe kasuwar Maru nan take .
Jami’in huda da jama’a na rundunar ‘Yansandar Jihar zamfara, ASP Yazidu Abubakar ya tabbatar da faruwar harin, kuma ya bayyana wakilinmu cewa, yanzu haka jami’an tsaro ne ke tsare da fadar Sarkin kuma mun baza jami’an tsaro lungu da sakon na Karamar Hukumar don tabbatar da tsaro.