Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya (NTRCN), Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya mika sakon taya murna ga Oba Alhaji Rashidi Adewolu Ladoja, saboda nadinsa a matsayin sabon Olubadan kuma sarki na 44 a kasar Ibadan.
Sarkin, a cikin wani sako da ya fitar a safiyar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun Alhaji Sai’idu Maccido, Sakataren Majalisar Sarkin Musulmi, ya yaba wa magajin marigayi Oba Akinloye Owolabi Olakulehin, wanda ya rasu a ranar Litinin, 7 ga watan Yuli, kuma aka yi jana’izarsa a ranar 8 ga Agusta, 2025.
- Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface
- Safarar Yara: Gwamnatin Adamawa Ta Haɗa Yara 14 Da Iyayensu Da Aka Ceto A Anambra
Naɗin Ladoja, wanda majalisar naɗin sarakuna ta Olubadan ta yi kwanan nan, ya tabbata ne a lokacin da Gwamna Seyi Makinde ya kai masa gaisuwar ban girma a gidansa na Bodija da ke Ibadan a ranar Laraba 20 ga Agusta, 2025.
Da yake yabawa da irin dimbin gogewar da Oba Ladoja ke da ita, wanda ya kasance dan kasuwa, manomi, tsohon dan majalisar tarayya, kuma tsohon gwamnan jihar Oyo, Sarkin Musulmi ya bayyana kwarin guiwar sa na cewa, lallai zai yi aikin abun yabawa a sabon mukaminsa na Olubadan na kasar Ibadan.
Sarkin Musulmi ya kuma taya Gwamnan Jihar Oyo, Engr. ‘Seyi Makinde murna, da kuma yi masa fatan alheri duba da yadda ya amince da sarkin da jama’arsa suka bukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp