Sarkin Samari Ya Yaba Wa Shugaban Karamar Hukumar Lokoja

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

Sarkin Samarin Lokoja, Alhaji Muhammed Adamu Alfa, ya jinjina wa shugaban karamar hukumar Lokoja, Alhaji ( Hon) Muhammed Danasabe Muhammed a bisa dimbin nasarorin da ya samu cikin kwanaki 100 a ofis, a matsayin shugaban karamar hukumar.
Alhaji Alfa, ya yi yabon ne a yayin da yake zantawarsa da wakilinmu.
Sarkin Samarin na Lokoja, wanda shi ne shugaban kungiyar masu sayarwa da kuma rarraba jaridu da mujallu na Jihar Kogi (Kogi State Newspapers & Magazines Sallers & Distributors Association) ya ce Hon Muhammed Danasabe, a cikin kwanaki dari da yayi kacal a matsayin shugaban karamar hukumar Lokoja, ya inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Lokoja ta hanyar samar musu da abubuwan more rayuwa da samar da tsaro da dai sauransu.
Alhaji Muhammed Adamu Alfa kazalika, ya zayyano dimbin nasarorin da shugaban karamar ya samu da suka hada da giggina rijiyoyin burtsatsi a lungu lungu da sako sako na karamar hukumar da samar da tsaron hadin gwiwa mai suna ‘Operation Lungu Lungu’ domin dakile ayyukan laifuka a fadin karamar hukumar da samar da motoci ga jami’an tsoro da kyautata danganta tsakanin bangaren majalisa dana zartaswa da kuma nade naden mukaman siyasa ga yayan jam’iyyar APC wandanda suka bada gudunmawarsu wajen ci gaban jam’iyyar,har ma da wadanda mambobin jam’iyyar ba..
Akan haka nema, Sarkin Samarin na Lokoja ya yabawa Hon Muhammed Danasabe Muhammed a bisa wadannan nasarorin daya samu, sannan yayi kira ga al’ummar karamar hukumar Lokoja da su ci gaba da baiwa shugaban goyon baya domin bashi kwarin gwiwar ci gaba da samar da romon dimukradiyya ga jama’a.
Ya kuma kara da cewa kungiyarsu ta masu sayar da jaridu da mujallu suna jaddada gpyon bayansu ga salon shugabancin Hon Muhammed Danasabe Muhammed, inda a karshe yayi roki shugaban karamar ta Lokoja daya sanya su cikin wadanda zasu ci gajiyar romon dimukradiyya.

Exit mobile version