Connect with us

TATTAUNAWA

Sarkin Tikau Ya Na Kokarin Dakile Rikici Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Yobe  — Madakin Tikau

Published

on

Magajin Tikau

A madadin Mai Martaba Mai Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Girema, Madakin Tikau, Alhaji Musa Lawan (Nangere), sannan kuma jigo a  jamiyar APC a  jihar  Yobe, ya  bayyana yadda wasu daga cikin matakan da masarutar ke dauka wajen dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin. Ya bayyana hakan, da wasu batutuwan a tattaunawar da  wakilin  mu  a  jihar  Yobe-  Muhammad  Maitela  ya  yi  dashi  a  fadar  Mai Tikau, ga yadda firar ta ke.

 

Ranka shi dade Madaki, ga shi daminar bana ta kankama, wane kira za ka yi ga manoma da makiyaya? Bisimillahi rahamani rahim, da farko za mu yi wa Allah godiya kamar yadda kuka yi tattaki ku ka zo nan a daidai wannan lokacin wanda damina ta matso, da kokarin sanin wadane matakai ne masarutar Tikau ta ke dauka wajen dorewar zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

A wajen mu gaskiya mu na hamdala, saboda Mai Martaba Mai Tikau ya yi bayani kuma kusan bayanin ma  ni  nayi  da  bakina  a ranar Sallah- a madadin shi, kuma mun yi Sallar ma mun yi cikin ruwa, wanda hakan ya kara tunatar damu cewa lallai lokacin damina ya kankama. Kuma mun san cewa abubuwan da ke faruwa a wasu sassan kasar nan.  Kuma  Mai  Martaba ya sani cewa  yawancin rikici tsakanin manoma da makiyaya, kan gonaki ne wanda ya samo asali daga burtali, yayin da kusan kowane bangaren kasan  nan,  matsalar  kenan, inda za ka tarar manoma sun handame wadannan burtalolin.

Inda hatta inda dama babu shanun a kasar, amma dai akwai taswirar su kuma kowa ya san da hakan. Bugu da kari kuma, a baya mutane ba su yi yawa kamar yanzu ba, wanda ake samun yawan jama’a na ninkuwa tare da jawo bukatar fadada gonakai da wuraren noma, inda wani zubin har inda za ka yi noman ma babu. Wanda  idan  ka  lura  a  yanzu duk babban gidan da ka tarar a kauye, mai dauke da mutum 20, zai yi wahala a gidan ka sami mutum daya da gona mai kunya 100, saboda idan gadone duk an kacancana. Bisa ga hakan ya jawo bukatar gonakin noma ta yi yawa; da zarar ka hango f ili  komai  kankantar  shi, sai ka je ka gyara kai ma ka mayar dashi gona, wannan ne ya tikasta dole mutane su ka rinka cinye dukan dazuzukan da ake dasu hadi da burtalolin.

Wanda zancen da ake ciki yanzu, itace su na neman su f i  hatsi  tsada,  saboda  yadda ya kasance itacen da a da za ka  je  bayan  gari  ka  tsinto a dafa abinci da shi, ya yi wahalar gaske, duk an riga an gama da shi. Bisa  la’akari  da  wadannan sauye-sauye  tare  da  rigingimun da su ke son kawowa, ya jawo Mai Martaba, Mai Tikau ya yi kokari, wanda a wannan masaruta ta mu, babu  wani  gurin  lamba  da  ba mu je mun yi dashen itatuwa ba,  inda  kimanin  shekaru 11, kowace shekara mu na aikin  dashen  itatuwa,  ta hanyar bin kowace gunduma a wannnan masaruta ta na umurtar mutane su je su  dasa  itacen da  kansu  a cikin  gonakansu  da  wuraren musamman,  tare  da  wayar da su kan cewa zai taimaka musu wajen zamantakewar yau da kullum.

Ta wace hanya Mai Martaba ya ke dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya? Bisa ga gaskiyar magana, Mai  Martaba  bai  tsaya ba,  kullum  ya  na  kan  irin wannan aikin tattaunawa da kiran makiyaya da manoma don ganin ba a samu sabani a tsakani ba, kuma wadannan matakan sun taimaka wajen dakile faruwar husuma a tsakanin bangarorin. Kuma abin bai tsaya nan ba, ko da Bakarkare (mazauna yankin) ya ke da dabbobi to shima makiyayi  ne,  kamar  yadda Bafulatani ya ke da shanu shima makiyayi ne, haka shima Bahaushe matukar ya na da dabbobi to makiyayi ne, mutumin da yake da shanu ya shiga ayarin makiyayi, kuma dole ne ake hadawa wuri guda tare da manoma don ganin an samu fahimtar juna a wannan masaruta ta Tikau.

Saboda haka, babban abinda Mai Martaba ya yi la’akari dashi shi ne, duk cikar jama’ar masarautar shi hakki ne a kan sa ya ga kowa ya  na  zaune  lafiya  da  dan uwan shi, saboda babu yadda za a ci  gaba idan babu  zaman lafiya  da  fahimtar  juna.  Don haka  Mai  Tikau  ya  na  kira ga al’ummar masarautar shi su maida hankali kada su rika bari shaidan ya shiga tsakanin su da junan su, su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurin ki daya.

Sannan idan mun kula, a shekarun  baya,  babu fada tsakanin makiyayi da manomi, kowa ya na ganin mutuncin kowa kuma kowanen su ya na girmama junan su. Wanda a da can, da zarar manomi ya cire amfanin gonar shi, sai ya bar wa makiyaya harawa da karmami su cinye ba a fada babu harara. Kuma a idon mu a baya mun sha ganin makiyayi zai zo muna girbin dawa suna yanka ana tarewa shanun su suna bin baya suna cin karmamin lokaci, kuma ba a maida komai ya zama kudi ba, amma a yanzu kara ma ya zama kudi, harawan gyada ta zama kudi, babu abinda zaka jefar hatta kashin shanun ma ya zama kudi.

Saboda haka dole ne a samu wadannan rigingimun, don haka dole ne a tashi tsaye a wayar da kan mutane a tuna musu yadda rayuwa take a shekarun baya, idan zai  yuwu a koma kan tafarkin baya, duk da ba zai yuwu ba, amma dai a kwatanta, kuma mu  a  kasar  mu  ta  Nangere ba mu da makobtan da mu ka sani sai Fulani.

Yallabai, yanzu mi ye mafuta kan wannan tirka-tirkar? A  tawa  fahimta,  mafita sannan  kuma  duk ita ce mu a wannan masaruta, mu kalli yanayin zamantakewar da take tsakanin manoman mu da makiyayan  mu,  abin  nufi,  a yi zama irin na da. Saboda Bafulatani shi ne makobcin Bakarkare, shima Bakarkare ba shi da na kusa dashi kamar Bafulatani.  Duk  da  yanzu lokaci  ya  canza,  abubuwa su na nema su lalace. Amma batun  burtali,  Sarakunan ba za  su  iya  yin  komai  a  kai  ba sai dai gwamnati; ta tarayya da  ta  jihar,  domin  su  ne nauyin  daukar  matakai  ya rataya bisa wuyan su. Abin ya  fi  karfin  masaruta,  ba za ta iya kewaye gonakin mutane ta ce ba za a noma ba, sai ka ga an kai ta gaban gwamnati ayi ta jele da ita, amma ita gwamnati ita za ta yi kayan ta.

Amma kuma duk da hakan, a matsayin masarutar Tikau ta na iya kokarin ta, kuma a gaskiya Mai Martaba ya cancanci a yaba masa ta irin yadda ya ke kokarin wanzar da  zaman lafiya,  a  fuskan addini, a zamantakewa da sauransu, idan yanzu ka duba masarutan Tikau ina tsammani ba za ka samu wani garin Lamba (mai gari) wanda za ka tarar babu makarantar babu Islamiya ba a ko ina yadda ake Zakka da  Wakafi  nan  dashi  ake biyan malamai na Islamiya nan, har ma matan aure da suke masarutar Tikau ba a bar su a baya ba wajen neman ilimin addini ba, kuma  wannan  duk  jajircewa Sarki ce.

A karshe, kullum mu na kokari wajen bai wa Sarkin Tikau shawarwarin da su ka kamata, kuma wanda zai taimake shi, saboda yadda mu ke tare da shi a kowane  lokaci  da  yanayi. Sannan kuma, a hakan, mu ka  zauna  da  mahaifin  shi, har Allah ya karbi ranshi gashi shi kuma mu na tare, in mun ga abinda ba daidai ba za mu gaya mashi kuma Alhamdulillahi ya na daukar shawarwarin mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: