Daga Bello Hamza,
Tun bayan hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Zazzau na 19 tare da kuma rasuwar wasu manyan masu rike da mukamai a masarautar Zazzau a ‘yan kwanain nan, Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya amince da sabbin nade nade tare da kuma daga darajar wasu masu rike da sarautun gargaji a masarautar kamar haka:
An daga darajar Malam Mansur Nuhu Bamalli daga Barde Kerarriyan Zazzau a halin yanzu shi ne sabin Magajin Garin Zazzau, mukamin da sabon Sarkin ya rike kafin ya zama Sarkin Zazzau.
Haka kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Zaria, Hon Abbas Tajjuddeen ya zama sabon Iyan Zazzau. Yayin da kuma Malam Shehu Tijjani Àliyu Dan Sidi Bamalli Barden Kudun Zazzau Hakimin Makera/Kakuri ya zama Barden Zazzau.
Yayin da kuma Malam Buhari Ciroma Aminu ya zama sabon Barde Kerarriyan Zazzau, an kuma daga likkafar Alhaji Idris Ibrahim Idris daga Barden Zazzau a yanzu ya zama Sa’in Zazzau, an kuma nada Alhaji Aminu Iya Saidu mukamin sabon Kogunan Zazzau shi kuma Alhaji Bashir Abubakar tsohon jami’in kwastam ya zama Barden Kudun Zazzau haka kuma an nada Maishari’a Munnir Ladan wanda kani ne ga marigayi Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan, tsohon Hakimin Kabala, a matsayin sabon Dan Iyan Zazzau.
Nan gaba za a sanar da ranar da za a gudanar da bikin kaddamar da su tare da yi musu nadi sabbin mukaman na su.