Yayin taron manema labarai da aka gudanar da yammacin jiya Litinin 21 ga watan Agustan nan, a sabon ofishin shirya bikin baje kolin kasa da kasa na Sin, a fannin cinikayyar harkokin ba da hidima wato CIFTIS, an bayyana cewa, a bana za a gudanar da baje kolin fannin tsakanin ranaikun 2 zuwa 6 ga watan Satumba dake tafe a birnin Beijing.
Baje kolin na shekarar 2023, na da taken “A kara bude kofa don bunkasa ci gaba, da hadin gwiwar cimma moriyar juna domin gaba”, kana adadin sassan kasa da kasa da za su shiga a dama da su a bikin na bana ya karu da kaso sama da 20 bisa dari. Har ila yau a halin da ake ciki, an kammala dukkanin shirye shiryen gudanar baje kolin cikin nasara.
An dai tanaji filin da ya kai kusan sakwaya mita 155,000 domin gudanar da baje kolin, an kuma tsara tattaunawa kan muhimman fannoni 9, da gudanar da ayyuka a sassa 6, ciki har da taron kasa da kasa game da cinikayyar harkokin ba da hidima.
A bana ne kasar Sin ta dawo da gudanar da nau’o’in baje koli da take shiryawa a zahiri, sabanin ta yanar gizo, kuma a bana baje kolin kasa da kasa na Sin, a fannin cinikayyar harkokin ba da hidima ya gabatar da karin takardun gayyata ga mahalarta, inda ya mayar da hankali ga janyo hankalin sassan kasa da kasa, da kyautata jagoranci da kwarewa.
Ya zuwa ranar Lahadi 20 ga watan nan, sama da kamfanoni 2,200 ne suka sanar da aniyar su ta halartar baje kolin dake tafe. Kaza lika a wannan karo an gayyaci karin kamfanonin ketare, da hukumomin kasa da kasa, yayin da kasashe da hukumomi daban daban har 75, suka sanar da burin su na baje kolin hajojin su, bisa sunayen gwamnatocin su, ko helkwatar su. Adadin da ya karu, idan an kwatanta da wanda ya gabata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)