Sassan ma’aikatun gwamnati dake karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin sun gudanar da shawarwari da tsare-tsare 12,480 da wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da mambobin kwaminitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin suka gabatar a shekarar 2023, kamar yadda kakakin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a ranar Alhamis.
Sassan sun yi amfani da shawarwari 7,955, wanda ya kai kashi 95.7 cikin dari na dukkan shawarwarin da aka gabatar, da tsare-tsare 4,525 wato kashi 96.5 cikin dari na dukkan tsare-tsare da aka gabatar, a cewar kakakin, Xing Huina a taron manema labarai.
Xing ta bayyana cewa, sassan sun fitar da matakai sama da 2,000 bisa wasu shawarwari da tsare-tsare guda 4,700 a shekarar da ta gabata, tare da samun ci gaba wajen inganta ci gaban tattalin arziki da tabbatar da kyautatuwar rayuwar jama’a. (Muhammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp