Daga Rabi’u Ali Indabawa
A ci gaba da yaƙin da ƙasar Saudiyya ke jagoran na lugudan wuta akan al’ummar ƙasar Yamen.
Majalisar Ɗinkin duniya ta sanya Saudiyya a jerin ƙasashen da za ta fitar waɗanda ke yi wa yara ƙanana kisan kiyashi a lokutan yaki, saboda rawar da take takawa a gamayyar da take jagoranta wajen yaƙin Yemen.
Sanarwar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ta ce ayyukan gamayyar ƙasashen sun jawo mutuwar yara 638 a shekarar 2016, ta kuma zargi gamayyar da kai hare-hare 38 kan makarantu da asibitoci, inda ahalin yanzu ake daɗa samun yawaitar jama’a saboda ƙarancin magani da likotoci.
Sai dai gamayyar ƙawancen ƙasashen ta yi watsi da batun, cewa tana sane take kai hare-hare kan fararen hula da kuma gine-gine.
Wani rahoto mai kama hakan da Malisar Ɗinkin Duniya ta fitar yana nuni da cewa, an kashe fiye da mutum 8,530, waɗanda kashi 60% daga cikinsu fararen hula ne, sannan kuma hare-haren da ake kai wa da jiragen sama sun jikkata mutum 48,800 tun daga watan Maris ɗin 2015.
An bar mutum miliyan 20.7 cikin tsananin buƙatar agajin gaggawa, al’amarin da ya jawo tsananin bukatar abinci da ba a taɓa ganin irinsa ba a.
Sakataren Malisar Ɗinkin Duniya na fitar da rahoto kan yara da yaƙe-yaƙe wanda ke ɗauke da jerin sunaye na wasu ɓangarori da ake zargi da take haƙƙi a ko wacce shekara.
Daftarin rahoton na baya-bayan nan na cewa: “A Yemen, ayyukan gamayyar ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya jawo kashe yara har 638, kuma an samu wannan adadi ne bayan an tabbatar da cewa ita ke da alhakin kai hare-hare 38 a makarantu da asibitoci a shekarar 2016.”
Haka kuma rahoton ya nuna ƙarara cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi amanna cewa gamayyar ƙasashen “Ta fara ɗaukar matakan da suka dace a lokacin da ake haɗa Daftarin rahoton don tabbatar da bai wa yara kariya.”
Wakilin Saudiyya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Abdallah al-Mou’allimi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai ce komai ba kan rahoton har sai sakataren Majalisar António Guterres, ya amince da shi a hukumance nan gaba cikin wannan watan na Oktoba.
Shi ma mai magana da yawun MajalisarƊinkin Duniya Stephane Dujarric ya ƙi cewa komai kan Daftarin rahoton. Shugaban ƙungiyar Saɓe The Children mai fafutukar ƙwato wa yara haƙƙoƙinsu Helle Thorning-Schmidt, ya ce, “Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi abin da ya dace don ƙwatowa yaran da suke yankunan da ake yaƙi haƙƙoƙinsu.
“Hakan zai sa duk ɓangarorin da aka sanya a wannan jeri da ma duk wani ɓangare da ke da hannu a yakin Yemen shiga taitayinsu, da ma ƙasashen da ke goyon bayansu ba su makamai.”
A bara dai an cire gamayyar ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta daga jerin sunayen da aka fitar na shekarar 2015, duk kuwa da ƙorafin da ƙungiyar Saɓe The Children ta yi.