Rabiu Ali Indabawa" />

Saudiyya Ta Rufe Makarantu Don Rigakafin Coronavirus

Kasar Saudiyya ta dauki matakin rufe makarantu a yau Litinin a matsayin rigakafin yaduwar cutar Coronavirus.

A cewar hukumomin kasar, za a rufe makarantun ne har illa mashaAllahu.

Makarantun sun hada da kanana har zuwa jamioi, da na gwamnati da kuma masu zaman kansu a duk fadin kasar.

Wannan lamarin ya shafi har da masu karatun Islamiya a cikin masalatai.

An dauki matakin ne don kare malamai da dalibai.

Kasar ta kuma dakatar da yan kasarta, da wadanda ke zaune a kasar daga tafiya wasu kasashe 9 saboda fargabar yiwuwar kwaso cutar.

Ta kuma hana wadanda suka ziyarci kasashen cikin kwannaki 14 da suka gabata shigowa cikin kasar.

Kasashen dai sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait, Bahrain, Lebanon, Syria, Korea ta Kudu, Masar, Italiya da kuma Iraqi.

Hakan na faruwa ne bayan da aka rufe masallatan Harami na Makkah da ke Saudiyyar domin tsaftace su, yayin da Coronavirus ke ci gaba da yaduwa.

Jim kadan bayan hakan dai an bude masalatan don gudanar da sallar Jummaar da ta gabata.

Kazalika an maido da yin dawafi a dakin Kaaba ga masu ibada na cikin gida kawai.

 

Exit mobile version