Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar Saudiyya ta sanar da ɗaukar matakin hukunta duk wanda ya nemi yin aikin Hajji ba tare da izini ba, ko kuma wanda ke taimaka wa irin waɗannan mutane.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya (SPA) ya bayyana, hukuncin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Dhul-Qa’adah har zuwa 14 ga watan Dhul-Hijjah, wato kafin da lokacin fara aikin Hajji.
- Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
- An Kammala Horon Hadin Gwiwa Tsakanin Sojojin Saman Sin Da Masar Cikin Nasara
Duk wanda aka kama yana ƙoƙarin shiga Makkah ko yin Hajji ba tare da izini ba, zai fuskanci tarar Riyal 20,000 na Saudiyya (kimanin Naira miliyan 7 ko dala $5,332).
Har ila yau, wanda ya nemi bizar ziyara domin ya yi niyyar yin aikin Hajj ba tare da izini ba, za a ci shi tarar Riyal 100,000 (kimanin naira miliyan 26 ko dala $26,661).
Haka kuma, duk wanda ya ɗauki masu bizar ziyara zuwa birnin Makkah ko wuraren ibada a lokacin aikin Hajji, za a yanka masa wannan tarar.
Wanda ya ba su masauki a otal, gida, ko wani wurin zama shi ma zai fuskanci irin wannan hukunci.
Duk wanda ya je aikin Hajji ba tare da izini ba ko dan ƙasa ne ko wanda ya daɗe fiye da lokacin zama za a kori mutum zuwa ƙasarsa tare da dakatar da shi daga shiga Saudiyya na tsawon shekaru 10.
Hukumomin shari’a za su kuma karɓi motocin da aka yi amfani da su wajen safarar waɗanda ba su da izinin yin aikin Hajji, musamman idan motocin na masu laifin ne.
A wani labari da ya shafi aikin Hajji, Hukumar Hajji ta Ka6sa (NAHCON) ta sanar da cewa jigilar mahajjatan Nijeriya na shekarar 2025 zai fara ne daga ranar 9 ga watan Mayu.
A cewar wata sanarwa da Daraktar Watsa Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar ta ce mahajjata 43,000 ne suka riga suka biya kuɗin Hajji a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp