Shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau na tafe da wani sako na wata baiwar Allah inda take neman shawara daga wajen ma’abota wannan shafi.
Sakon na ta ya fara da cewa; “Ina da saurayi wanda muka yi alkawarin aure tsawon shekara guda, kuma ya amince da zai jira ni har na kammala karatuna na sakandare, kuma mahaifiyarsa ta san da hakan. Ya nuna mun babu wata ‘ya mace da yake so sama da ni, sai dai kuma yana kula wasu ‘yan matan daban, mahaifiyarsa ta sha yi masa magana kan cewa; idan ba ni yake so ya aura ba ya sanar da ni da wuri tun kafin abu ya yi nisa, amma ni bai taba fada mun ba. Duk ranar da na gan shi da wata na yi masa magana sai ya ce; ai ya fi so na sama da wata. Dan Allah ina so a ba ni shawara, na rabu da shi na samu wani ko kuwa da gaske so na yake yi?”.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin ma’abotansa game da wannan batu; Ko me za a ce akan hakan?, Idan har ta amince da shi, wanne irin matsaloli ne ka iya afkuwa a gaba?. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jahar Jigawa:
To magana ta gaskiya wannan alkawari da ku ka yi da shi ba lalle ne ya cika ba muddun baki hakura da bukatar ki ba ta kammala karatu ba, to komai zai iya faruwa kuma aure ma ai ba zai hana kammala karatu ba, don ya kamata ki sake nazari, domin gudun yin da-na-sani. To duk amincewar da tayi da shi ba zai zama madogara gare ta ba, domin mutum ne dan Adam zai iya canzawa a kowane lokaci, don haka ya kamata tayi tunani ta nemawa kanta mafita, domin gudun kar tayi “fargar jaji”. To shawara ita ce; ya kamata mu san muhimmancin alkawari da kuma matsayinsa a addinin musulunci, don haka mu daina daukar alkawarin da muka san ba za mu iya cikawa ba, domin Allah zai tambaye mu, kuma ya kamata mu sani duk abun da ka yi wa ‘yar wani kai ma za a yi wa ‘yar ka, su kuma iyaye da ma ‘yan matan ya kamata suna amfani da lokaci domin a wasu lokuta idan kayi wasa da lokaci dole shi ma ya yi wasa da kai, don haka ya kamata duk lokacin da ‘ya’yansu suka samu mijin aure nagari a daina cewa sai an kammala karatu domin ana iya kammalawa a gidan miji, daga karshe nake addu’ar Allah ya shirye mu gaba ki daya.
Sunana Fadila Lamido Jihar Kaduna:
Wannan kawai mayaudari ne, bakida tabbacin abin da yake gaya miki baya gayawa wata bayan ke, dole a cikin ku akwai wadda zai yaudara, idan ke Allah ya sa akwai aure a tsakaninku sai ki ka ga ya aure kin, sai dai koda an yi auren mawuyacin abu ne ya daina hira da wasu matan tunda ya saba, idan kin jure hakurin ganin hakan kafin aure Allah ya baki hakurin jurewa bayan auren. Shawarata ga maza masu irin wannan dabi’ar idan har sun daidaita da yariyar da suke son aura tana sonka kana sonta ya kamata ka tsaya anan din ne kawai dama ai neman aure ka je kuma ka samu wadda kuka daidaita to mene ne amfanin zuwa gun wata kuma?
Sunana Anas Bin Malik, Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:
A gaskiya duk namijin da ya nuna miki hali irin wannan, shakka babu ya canja akalar zuciyarsa zuwa wata daban ba ke ba, kawai dai ba zai iya fitowa ya fada miki hakan ba ne, duba da cewa maganar ta kai ga Iyaye. Dan haka rabuwa da shi ya fi maki alkairi, tunda ya kasa cika alkawarin dake tsakaninku, kuma ya kasa boye miki soyayyarsa da wasu ‘yan matan daban bayan ke, idan kuwa ki ka kuskura ku ka ci gaba da soyayya da shi a haka, ba za ki taba zama da farin ciki a zuciyarki ba. Domin a soyayya cika alkawari dai jigo ne, matukar babu shi kuwa dole a fuskanci zargi, cin amana, rashin kyautatawa da makamantansu. Su kuma mazan da suke da irin wannan hali, ina mai basu shawara da su ji tsoron Allah su sani, Allah ya hana mutum ya cutar da dan uwansa, ta kowace fuska.
Sunana Maryam Abdullahi, Jihar Kano:
Gaskiyar magana ita ce; ta rabu da shi, sabida ba lallai da gaske yake ba furucin da ya yi mata, alama ce ta mayaudari, ba mamaki su ma wadanda ta ganshi da su din hakan ya fada musu, Allah kadai ya san wanne irin dadin baki yake yi muau. Kuma ban da abinki kamar ba mace ba, ai za ki iya ganewa in yana sonki ko baya sonki, duk namijin da zai iya kule-kule har ma ki rinka gani baya shayinki to, ai alama ce ta ke din ma ba komai ba ce, kuma ko babu ke yana da wasunki. Ni dai shawarata kawai ta hakura da shi ta maida hankali akan karatunta kamar yadda iyayenta suke bukata, babu ma wani amfanin kula saurayin tunda ta san abin da yake gabanta, idan ta kammala karatun sai ta fara soyayyar hakan ina ganin zai fi.
Sunana Abbale Ismail, Jihar Kano:
Ni dai a gaskiya shawara ta ita ce; duk abin da ka ga iyaye sun tsawatawa da bai bari ba to, ban ga abin da zai sa ya hanu ba, dan haka na fi ganin kawai bata miki lokaci zai yi ki hakura da shi ki nemi Allah ya kawo miki wanda ya fi shi wanda da gaske yake ba yaudararki zai yi ba, to idan kin amince da shi ta iya yuwa ki ji watarana an ce miki an daura mishi aure da wata, ko kuma ki ta fuskantar wulakanci kala-kala. Shawarata ita ce akan ‘yan wana maza mu sani duk abin da ka yi wa ‘yar wani, inidai Allah ya baka tsawan rayuwa sai an yi wa kanwarka ko ‘yarka, haka manzo Allah ya ce, Allah ya ba mu ikon gyarawa, Ameen.
Sunana Rabi’atu Abdullahi, Jihar Kano:
Toh dai indai yana sonta kamar yadda yake fada da kuma alkawarin da yayi mata ita ma kuma tana sonsa tsakani da Allah toh ta jira shi zai cika mata alkawari ya aureta nan gaba. Tayi kyakkyawan zato a a kansa idan kuma aka samu akasi bai aure ta ba toh ta dauka kaddarar ta ce daga Allah kuma ba alkhairinta bane, sannan ta dage da addu’a wajen zabin ubangiji. Idan har sun san a karshe ba za su iya aurar wacce suka yi wa alkawari ba toh tun farko su daina yi wa mata haka, sanna suke barinsu suna kulla sauran wa ‘yanda za su fito su nuna suna son su, su daina bata musu lokaci su fada musu gaskiya ban da yaudara.
Sunana Lawan Isma’il Lisary, Jihar Kano, Karamar Hukumar Rano:
Abin da zan iya cewa anan shi ne wannan ba damuwa bane duba da ita ta amince shi ma saurayin ya amince uwa uba kuma iyayensu duka sun sani, sannan ta sani koda ta ga yana kula wasu ‘yan matan wannan ba dalili ne da zai sa ta ce zai gujeta bane, domin koda aure suka yi halinmu ne na maza kula mata, koda yake ba dukkanmu ne muke haka ba. Matsala ba fatan samunta ake ba iyakaci dai ta guji duk wani abu da ransa zai baci koda ta ga yana kula wasu ‘yan matan, sannan shi ma ya ji tsoron Allah ya tuna nauyin alkawarin da ya daukar mata. Shawarata anan ita ce; duk saurayin da ya san ba zai iya rike alkawari ba ka da ma ya fara daukar alkawarin, sannan kuma ai ita ce abar tsoroma duba da za ta iya kare karatunta canjashi da wani ni a nawa ganin wannan ba matsala bane. Allah ya sa mu dace.
Sunana Habiba Tijjani, Jihar Kano:
Shawarar da zan bayar ita ce; kawai ta rabu da shi ta ci gaba da addu’a Allah ya fito mata da wanda ya fi shi zama alkhairi. Idan ta amince da shi hankalinta ba zai taba kwanciya ba suna iya fuskantar matsaloli ta rashin yarda. Shawarar da zan ba su ita ce; su rike gaskiya da rikon amana su sani so duk abin da ka yi wa ’yar wani kai ma za a yi wa taka.
Sunana Musbahu Muhammad, Gorondutse Jihar Kano:
Ta rabu da shi tayi Addu’a Allah ya fito mata da wanda ya fishi Alkhairi, idan ya amince to dole ta shirya ganinsa da ‘yammata kala-kala. Bai kamata namiji ya zama mayaudari ba, saboda yaudara haramun ce kuma idan shi aka yi masa ba zai ji dadi ba.