A daidai lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ke shirye-shirye mika mulki ga sabuwar gwamnati ma’aikata musamman masu rike da mukaman siyasa suna fuskantar rasa ayyukansu saboda sabbin nade-naden da za a yi a sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, kamar dai yadda binciken da LEADERSHIP HAUSA ta yi.
Duk da yake lamarin rasa aiki ba wani sabon abu ba ne, musamman ganin gwamnati mai kamawa za ta nada mutanen ta ne da za su yi aiki tare, amma fargarbar da ke tattare da rasa aiki ya kara kamari a tsakanin masu rike da mukaman siyasa a wannan lokacin.
- Wasu Ke Neman Bata Mana Suna Kan Rikicin Shugabancin APGA – INEC
- Gwamnati Ta Amince Da Sabbin Manufofin Bunkasa Samar Da Motoci A Nijeriya
Binciken mu ya nuna cewa, rasa ayyukan zai dangantaka ne da irin tsare-tsaren da yadda sabuwar gwamnatin ta shirya gudanarwa da ayukan da za ta sa a gaba da zaran an rantsar da ita.
A baya, wasu sabbin gwamnatin da aka yi su kan zabi kawar da kowa ne da ya yi aiki da gwamnati mai barin gado wanda hakan ke haifar da rashin ayyukan yi mai dimbin yawa yayin da wasu gamnatin ke zabar samar da canjji a sannu da hankali har a kai ga canza wadanda suka yi wa tsohuwar gwamnati aiki a samar da sabbin mutane da za su yi aiki da sabuwar gwamnatin gaba daya.
Lamarin a wannan lokacin ya za da sabon salo musamman ganin kasar na fuskantar matsalolin tattalin arziki, abin da ya sa ake ganin gwamnatin na Bola Tinubu za ta nemai aiwatar da rahoton kwamitjn nan na Stebe Oronsaye wanda ya bayar da shawarar sake fasalin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, akalla kwamitin ya nemi a hada wasu ma’aikatu a wuri daya ko kuma a rusa wasu ma’aikatan ba tare da wata lokaci ba, wannan aiki kuma ana ganin zai shafi akalla ma’aikata fiye 102 yayin da kuma za a umarci wasu ma’aikatan su fuskanci nema wa kansu kudaden shiga.
Nijeriya na ci gaba da farfadowa daga rikicin karayar tattalin arziki da aka fuskanta a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, da matsalar da cutar korona ya haifar a shekarar 2020 wadanda suka tagayyara tsarin tattalin arzikin kasa.
Yayin da gwanmati ke kokarin ganijn ta sauke nauyin da ke a kanta na biyan albashi da sauransu, ta kuma tilastawa kanta karbar basuka don gudanar da manyan ayyuka akwai manyan fargaban cewa nauyi zai yi wa gwamnati mai kamawa yawa ta yadda ba za ta iya biyan hakokin da ke a kan ta ba na al’umma Nijeriya kamar yadda ta yi alkawari.
In har gwfamnati mai kamawa ta bata yanke shawarar rage ma’akatun gwamnati, hakan zai kai ga rasa ayyukan yi a tsakanijn ‘yan Nijeriya, abin kuma da zai fi shafar masu mukaman siyasa saboda ana ganin su a matsayin cima zaune.
Amma kuma ga dukkan masu mukaman siyasa ne za a iya kira da cima zaune ba, musamman ganin ana iya amfani da su wajen tabbatar da ayyukan gwamnati na cigaba daga gwamnatin da ke barin gado zuwa gwamnatin mai kamawa.
Abin kura kuma ba wai rasa aikin zai tsaya ne kawai a ikajn masu rike da mukaman siyasa kawai ba ne, lamarin zai iya sahafar wasu ma’aikatun gwamnati da ke fiuskantar matsalar rashin kudaden gudanarwa.
A wannan karon ana ganin fiye da ma’aikata 2,585 za su rasa ayyuansu a majalisar kasa da fadar shugaban kasa, a yadda abin yake ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari na da masu rike da mukaman siyasa 160 yayin da mataimakinsa Yemi Osinbajo ke da ma’aikata 80 wadanda ke taimaka masa a bangarori da dama.
A majalissar kasa kuma akwai ma’aikata na kaida 2,345 da suke yi wa ‘yan majalisa 469, sanatoci 109 ‘yan majaliisar wakilai 360, suna aiki ne a bangarori daban-daban don kawo wa ‘yan majalisar sauki a yayin db suka gudanar da ayyukansu. Ana iya samun kakrin mataimaka ga ‘yan majalisu in har shi dan majalisar yana neman karin masu taimakama masa wadnda kuma suna cikin wadanda za su rasa aiki a wannan lokacin na sauyin gwamnati.