Jam’iyyar APC ta yi kira ga Babban Lauyan gwamnatin tarayya, SAN Abubakar Malami da gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele, da su girmama umarnin kotun koli akan maganar sauya sabbin takardun kudade .
Shugaban APC na kasa, sanata Abdullahi Adamu ya ce, wannan kiran na daya daga cikin matsayar da gwamonin APC da kwamitin zartarwa na jam’iyyar suka cimma a taron su na gaggawa da suka gudanar a jiya lahadi a Abuja.
Adamu wanda ya shedawa manema labarai hakan jim kadan bayan kammala taron sirrin ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa baki acikin maganar don lalubo mafita akan matsalar da tsarin na sauya kudaden ta janyo.
A hukuncin da kotun koli ta yanke, ta umarci CBN da gwamnatin tarayya da su dakatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da takardun kudaden naira 200, 500 da 1000 har sai kotun ta yanke hukunci a ranar 22 ga watan fabrairu 2023.
Sai dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 16 ga watan janairun 2023 ya sanar da cewa, naira 200 ce kawai za ta ci gaba da zama halartacciyar takardar kudi da za a ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afirilun 2023, inda kuma tsohuwar takardun kudi na naira 500 da naira 1000 suka zama tarihi a kasar.
Gwamonin Kaduna, Kogi, Jigawa, Yobe, Zamfara, Filato, Ekiti, Neja, Kebbi, Gombe, Lagos da kuma na Nasarawa ciki har da mataimakan gwamnonin Imo da Katsina, duk sun halarci zaman ganawar sirrin.
Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu, shi ma ya halarci ganawar wacce aka shafe kimanin sa’o’i uku ana yi.