Yau Jumma’a 9 ga wata, ita ce jajibirin sabuwar shekara ta kasar Sin. Da karfe 8 na dare, agogon Beijing, jama’a daga sassa daban-daban na duniya, sun fara kallon shagulgulan Bikin Bazara da CMG ya shirya kamar yadda aka tsara. A bana, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Bikin Bazara a matsayin ranar hutu a majalisar wanda ya bai wa “Shagulgulan Bikin Bazara ” wani muhimminci a duniya.
Tun daga shekarar 1983, gidan talabijin na kasar Sin, CCTV, ya kan gudanar da wani gagarumin bikin al’adu da fasaha a kowace jajibirin sabuwar shekara, wanda jama’ar kasar Sin ke kira “Bikin Bazara”. Abubuwan dake kunshe cikin shirye-shiryen, da nau’in gabatarwa da fasahar shagulgulan “Bikin Bazara ” duk suna wakiltar matakin koli na nune-nunen talbijin na kasar Sin.
Shagulgulan Bikin Bazara na shekarar 2024, zai kiyaye ka’idar shagulgulan ” Bikin Bazara na jama’a” wanda ya baiwa talakawa daga sassa daban-daban na kasar damar zama jaruman shagulgulan bikin.
Shagulgulan Bikin Bazara na wannan shekara, ya gabatar da samfuran hotuna masu inganci daidai da fasahar zamani.
Haka zalika, shagulgulan Bikin Bazara na bana, shi ma bikin ne na duniya. A daren yau, fiye da manyan allunan talabijin na zamani dubu 3 dake watsa shirye-shirye da rahotanni kai-tsaye daga babbar tashar dake watsa shagulgulan ” Bikin Bazara ” na babbar tashar dake kasashe 49 da birane 90 na nahiyoyi shida na duniya, za su baiwa masu kallo a fadin duniya, wata damar kallon Bikin Bazara na kasar Sin gami da al’adun Sinawa cikin murnar farin ciki da annashuwa. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)