CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Shaidu Da Gaskiya Game Da Karyar Da Ake Bazawa Kan Xinjiang

by CRI Hausa
December 18, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Shaidu Da Gaskiya Game Da Karyar Da Ake Bazawa Kan Xinjiang
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ranar 15 ga wata, cibiyar nazarin manufofin kasa da kasa, ta masanan Amurka ta fitar da wani rahoto, inda aka yi zargi cewa, ana tilastawa ‘yan kabilar Uygur sama da dubu 500 a jihar Xinjiang yin aikin tsintar auduga na dole, a jiya Alhamis 17 ga wata, majalisar dokokin Turai ta zartas da wani kuduri, inda ta suka gwamnatin kasar Sin kan yadda take tilastawa ‘yan kananan kabilun jihar Xinjiang yin aikin dole.

Hakika wasu ‘yan siyasa wadanda ke yin adawa da kasar Sin suna daukar kokarin gwamnatin kasar Sin na samar da aikin yi ga al’ummun kabilu daban daban na jihar Xinjiang a matsayin tilasta yin aikin dole, domin shafawa kasar Sin bakin fenti, tare kuma da lalata huldar dake tsakanin kabilu daban daban na kasar Sin, da ma hana ci gaban kasar Sin.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan “samar da aikin yi ga al’ummun jihar Xinjiang”, da “rahoton binciken yanayin da ake ciki a jihar Xinjiang a bangaren samar da aikin yi” da sauran takardu, inda aka yi cikakken bayani kan hakikanin yanayin da ake ciki a jihar, da manufar samar da aikin yi ta jihar wato mutunta ‘yancin samun aikin yi na al’ummun jihar, da tabbatar da hakkin ‘yan kwadago na jihar, da makasudin samar da aikin yi ga al’ummun jihar wato samar musu taimako ta yadda za su yi rayuwa cikin farin ciki.
An lura cewa, a daidai wannan lokacin, da gwamnatin kasar Amurka ta wannan karo ke shirin kammala wa’adin aikinta, wasu ‘yan siyasa na kasar kamar Mike Pompeo suna gurgunta kasar Sin, wannan shi ne dalilin da ya sa aka sake baza karya kan batun Xinjiang.
Game da manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa kan jihar Xinjiang, da ci gaban da aka samu a jihar a bangaren kiyaye hakkin bil Adama, yawancin kasashen duniya sun nuna goyon bayansu, a bayyane an lura cewa, yunkurin wasu ‘yan siyasar kasashen yamma na yin adawa da kasar Sin, ba zai iya goge hakikanan abubuwan dake shafar kwanciyar hankali da wadata da aka samu a jihar Xinjiang ba, ko shakka babu, yunkurinsu na siyasantar da batun Xinjiang da tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin ba zai yi nasara ba.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Ya Kamata Mu Ci Gaba Da Raya Kauyuka Domin Karfafa Sakamakon Da Aka Cimma A Fannin Yaki Da Talauci

Next Post

Kasar Peru Ta Yarda Da Farfado Da Gwajin Allurar Rigakafin COVID-19 Ta Kamfanin Sinopharm

RelatedPosts

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

by CRI Hausa
29 mins ago
0

Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

by CRI Hausa
36 mins ago
0

Jiya Laraba, ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fidda bayanin...

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

by CRI Hausa
41 mins ago
0

Kakakin ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur...

Next Post
Kasar Peru Ta Yarda Da Farfado Da Gwajin Allurar Rigakafin COVID-19 Ta Kamfanin Sinopharm

Kasar Peru Ta Yarda Da Farfado Da Gwajin Allurar Rigakafin COVID-19 Ta Kamfanin Sinopharm

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version