A kullum, bukatar kifin Tarwada kara karuwa yake a Nijeriya, duba da irin muhimmancin da yake da shi wajen gina jikin Dan Adam tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin wannan kasa.
Sai dai, akwai kalubale wajen kiwon Tarwadar, koda-yake amfani da dabarun kimiyyar zamani da kasuwanci, za su taimaka wajen samar da makoma mai dorewa a wannan fanni tare damammaki masu yawan gaske ga masu yin kiwon ta.
- Ta Hanyar Tinkarar Wannan Muhimmin Batu Ne Kawai Za A Iya Inganta Dangantakar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Ba Jihohi Wa’adin Mika Sunaye Maniyyata
Har ila yau, a Nijeriya an jima ana kiwon Tarwada a gargajiyance, wanda akasarin masu yin wannan kiwo; masu karamin karfi ne, sannan ba sa iya samun kayan kiwo na zamanin tare da dabarun kiwon, don samun kasuwar da ta dace.
Hakan ya yi sanadiyyar samun karancin Tarwadar da kuma rashin samun kudaden shiga masu yawa, rashin sarrafa ta yadda ya dace da kuma rashin samar da kayan aikin adana ta, wanda hakan kan jawo wa masu sana’ar yin asara a wasu lokutan.
Duk da wadannan kalubale, har yanzu fannin na samar da damammaki da suka hada da raguwar talauci, samar da ayyukan yi da kuma kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa.
Baya ga kasancewar Nijeriya a matsayin kasa mafi yawan al’umma a Afirka, ta kuma kasance kan gaba a duniya wajen samar da wannan kifi na Tarwada, wanda aka kiyasta cewa; tana iya samar da Tarwada tan miliyan daya a shekarar 2021, wanda kudinta ya kai kimanin dala biliyan 2.6.
Haka zalika, a Nijeriya akwai matakai da dama da ake bi na kiwonta, domin samun wadatacciyar riba da suka hada da; kiwonta, sarrafa ta, kasuwancinta da yin amfani da ita da sauran makamantansu.
Don haka, kowane mataki daya daga cikin wadannan matakai, na da irin nasa kalubalen da kuma damammaki.
Bisa wani bincike da aka yi karkashin aikin kiwon Kifi na ‘FISH4ACP’, wanda ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta gudanar ya nuna cewa, Nijeriya na da akalla masu samar da Tarwada kimanin 285,000, inda kananan masu kiwon suka doshi kashi 60 cikin 100.
Bisa hadaka a tsakanin hukumar abinci ta duniya (FAO) da ma’aikatar noma da raya karkara ta yi a kwanakin baya, sun kaddamar da wanzar da kashin farko na bunkasa kiwon Tarwada; don samun gwaggwabar riba a Nijeriya.
A yanzu haka, Nahiyar Turai (EU), da kuma ma’aiktar bunkasa tattalin arziki ne ke tallafa wa wannan aiki na ‘Fish4ACP’ a Nijeriya.
Kazalika, wannan wani shiri ne wanda kungiyar Afirka da jihohin da ke bakin teku (OCAPS), suka kirkiro da shi domin bayar da nasu goyon bayan wajen samar da wadataccen abinci mai gina jiki, kara habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi, samar da damar kasuwanci da zuba jari da kuma karfafa yin gasa a wannan fanni.
A nasa jawabin yayin kaddamar da shirin a Abuja, wakilin hukumar FAO a Nijeriya; Fred Kafeero ya bayyana cewa, aikin zai taimaka wajen farfado da fannin kiwon Tarwada a Nijeriya tare da samar da abinci da kuma habaka tattalin arzikin ‘ya’yan wannan kasa baki-daya.
Kafeero ya kara da cewa, Nijeriya na da matukar muhimmanci da dabaru a cikin sauran kasashe, wajen bunkasa kiwon Tarwada da kuma habaka kiwonta, don samun riba mai yawan gaske.
Wata tawagar Nahiyar Turai (EU), ta kawo ziyara kasar nan domin taimaka wa da dabarun kiwonta, musamman domin lalubo da mafita kan kalubalen da masu sana’ar da kuma ‘yan kasuwa ke fuskanta a Nijeriya.
Frank Okafor ne ya jagoranci tawagar a wajen taron, wanda ya ce, kungiyar ta mayar da hankali ne domin taimaka wa Nijeriya da sauran kasashen da ke Afirka, don samun damar cimma muradunsu ta hanyar taimaka wa da kudade tare da samar da dabarun cin nasara a wannan fanni na kiwonta a dukkanin fadin Afirka.
Shi kuwa Babban Sakatare a Mai’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara, Dakta Ernest Umakhihe cewa ya yi, ma’aikatar ta mayar da hankali ne, don habaka kiwonta wanda ake sa ran za a kara samar da yawanta, domin samun wadatuwa da ta kai kimanin tan 250,000, don cimma bukatar da ake da ita a kasar tare da rage dogaron da ake da shi na shigo da ita daga kasashen ketare.
Bugu da kari, kara fafado da wannan fannin a Nijeriya, abu ne da ke bukatar hada karfi da karfe a tsakanin gwamnati, masu ruwa da tsaki, masu kiwonta, masu yin bincike da kuma masana’antu masu zaman kansu.
Kazalika, yin amfai da dabarun da suka kamata da kuma samar da dauki ga fannin, masana’antar kiwonta za ta iya bayar da gudunmawa wajen kara habakawa tare da bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.