Akawai abubuwan da suka zama wajibi ga dukkannin mai sha’awar fara yin noman Agwaluma ya fara tanada, musamman duba da cewa; fannin na daya daga fanninin aikin noma, musamman a kasar nan da ake samar wa wanda ya rungume shi kudaden shiga.
A nan ga jerin abububuwan da ya kamata mai sha’awar shiga fannin ya fara tanada kamar haka:
Samar Da Kyakkyawan Tsari:
Kafin ka fara yin nomanta, ana so ka tabbatar da ka tsara yadda nomanta zai kasance, musamman domin kauce wa yin asara bayan ka zuba jarinka a fannin.
Gyaran Gonar Shuka Ta:
Kafin ka shuka Irinta, ana bukatar ka tabbatar da kasar nomanta mai kyau ce.
Zaɓo Nau’inta Da Ya Dace:
A nan ana bukatar ka zabo daga cikin nau’ikanta abiyu, wato na Udara ko kuma na Agbalumo, inda ake iya gano su ta hanyar girmansu.
Amfanin na kai wa tsawaon shekara takwas kafin ta kammala girma, inda kuma aka kara habaka nau’insa, wanda zai iya girma bayan shekara uku.
Kazalika, akwai matakan da ake bi wajen yi mata girbi, wacce akasari ana girbe ta ne a watan Disamba.
Ana kuma shuka irinta ne, wanda idan manomi zai sayo Irin nomansa, sai ya tabbatar da ya sayo a gurin da aka fi sani, musamman don ya samu ingantacce kuma mai lafiya.