• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Tashar Binciken Sararin Samaniya Ta Lasar Sin, Mallakar Kasar Sin Da Ma Duniya Baki Daya Ce

by CMG Hausa
3 years ago
Samaniya

Kwanan nan, kumbon Shenzhou-14 dake dauke da ’yan sama jannati uku ya dawo doron duniya. Kafin wannan kuma, ’yan sama jannati na kumbon sun yi musayar aiki tare da takwarorinsu dake cikin kumbon Shenzhou-15, wanda aka harba ba da jimawa ba, daga nan kuma, tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin da ake kira “Tiangong”, ta shiga wani sabon mataki na fara gudanar da harkoki daban daban. Kafin wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta taba sanar da bude tashar ga dukkanin kasashe mambobin MDD.

An ce, tun daga shekarar 2016, kasar Sin ta tattara shirye-shiryen gwaji daga wajen kasashe mambobin MDD wadanda suke so su gudanar a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, kuma kawo yanzu akwai shirye-shirye 9 na kasashe 17, da suka hada da Switzerland, da Poland, da Jamus, da Italiya, da na wasu rukunoni 23 da aka sanya su cikin jerin shirye-shiryen gwajin kimiyya na farko da za a gudanar a tashar.

  • Kumbon Shenzhou-15 Na Kasar Sin Ya Hade Tashar Binciken Sararin Samaniyar Kasar

Darektar ofishin kula da harkokin sararin samaniya na MDD Simonetta Di Pippo, ta bayyana cewa, yadda kasar Sin ta bude kofar tasharta ta binciken sararin samaniya ya kasance wani muhimmin bangare na shawarar MDD ta “binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa”, kuma misali ne abun yabawa.

Sai dai idan an waiwayi baya, Amurka da sauran kasashen yamma sun yi kokarin kafa shingen hana harkokin binciken sararin samaniya da kasar Sin ta gudanar, har ma kasar Amurka ta kafa dokar hana hukumar NASA ta yi hadin gwiwa da kasar Sin, ta hana kasar Sin shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasa da kasa. Amma hakan bai hana Sinawa kokarinsu na binciken sararin samaniya ba. Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da shirin harba kumbuna masu dauke da mutane a ranar 21 ga watan Satumban shekarar 1992, al’ummar Sinawa sun shafe tsawon shekaru 30 suna kokari bisa karfin kansu, har ma hakarsu ta cimma ruwa.

Ci gaban harkokin binciken sararin samaniya na kasar Sin, ba kawai ya shaida karfin kasar a wannan fanni ba, har ma ya sa kaimin ayyukan binciken sararin samaniya na dan Adam baki daya. Yadda kasa da kasa ke hada gwiwa wajen aiwatar da shirye-shirye a tashar bincike ta kasar Sin, zai taimaka wajen tara fasahohi a wannan fanni, da ma ciyar da harkokin binciken sararin samaniya na dan Adam gaba zuwa wani sabon matsayi.

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin wadda ta bude kofarta ga kasa da kasa, za ta zama gida na ’yan Adam baki daya a sararin samaniya.

Kamar yadda babban mai tsara ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin, mista Zhou Jianping ya ce, “Aikin da tashar Tiangong ta sanya gaba shi ne, ya zama dakin gwaji na kasar Sin a sararin samaniya, don tallafawa manazarta kimiyya wajen gudanar da nazari da bincike, don amfanin ’yan Adam baki daya.”

A watan Fabarairun bana, hukumar kula da harkokin sararin samaniya na kasar Amurka (NASA) ta sanar da cewa, tashar binciken sararin samaniya ta kasar za ta daina aiki a shekarar 2030, wadda daga baya za ta fado cikin tekun Pasifik. Ta haka, muna iya hasashen cewa, nan da shekaru 8 masu zuwa, tashar Tiangong ta kasar Sin za ta kasance tasha irinta daya kacal ta dan Adam, wadda kuma za ta dauki babban nauyin binciken sararin samaniya. Muna da imanin cewa, tashar za ta hada karfin kasa da kasa, don amfanin dan Adam baki daya, a kokarinta na binciken sararin samaniya. (Lubabatu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
‘Yansanda Za Su Yi Binciken Harin Da Aka Kai Gidan Shugaban Kwamitin Yakin Zaben PDP A Ribas 

'Yansanda Za Su Yi Binciken Harin Da Aka Kai Gidan Shugaban Kwamitin Yakin Zaben PDP A Ribas 

LABARAI MASU NASABA

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.