A kwanakin baya, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton yadda ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta gudanar da wani aikin farfaganda a asirce a yayin barkewar annobar COVID-19. Bisa ga rahoton, Reuters ya gano wasu shafuka a kalla 300 da aka bude ta kafar sada zumunta na X (wato Twitter a baya), wadanda suka yi ta yada karairayi na shafa wa alluran rigakafi kirar kamfanin Sinovac na kasar Sin kashin kaji. Shafukan dai suna karkashin jagorancin sojojin kasar Amurka, kuma kusan an bude dukansu ne a shekarar 2020. An fi gudanar da aikin a kasar Philippines, baya ga wasu kasashe maso tasowa da ke tsakiyar Asiya da ma Gabas ta tsakiya ma da aikin ya shafa.
Sakamakon wannan aikin, mutane kalilan ne suka karbi rigakafin a kasar Phlippines, wato daga cikin mutanen kasar miliyan 114, kimanin miliyan 2.1 ne kawai aka yi wa cikakkun rigakafin. Kakakin tsohon shugaban kasar ta Phlippines Harry Roque, ya bayyana ta kafar sada zumunta cewa, “Sama da ‘yan kasar dubu 60 suka halaka sakamakon annobar, wadanda ta yiwu su tsira da rayukansu idan da ba bu wannan mummunan aikin farfagandan da aka gudanar a kan rigakafi na Sinovac.”
- Shugaba Xi Na Kasar Sin Ya Amsa Wasikar Da Mutanen Gundumar Jingning Suka Aika Masa
- Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Murna Ga Makon Yin Cudanya Tsakanin Matasan Sin Da Amurka
A hakika, rigakafin Sinovac rigakafi ne daya kacal da kasar Philippines ta iya samu a wancan lokaci. Bayan barkewar annobar, kasar Sin ta rungumi ra’ayin nan na “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya”, inda ta yi kokarin samar da gudummawar kayayyakin kandagarkin cutar ga sassan kasa da kasa, ta kuma sanar da bai wa dukkanin kasashen duniya damar yin amfani da alluran rigakafin da ta hada idan ta kammala nazarinta, don tabbatar da kasashe masu tasowa sun iya samun rigakafin da suke bukata. A watan Faburairun shekarar 2021, rukunin farko na gudummawar alluran rigakafin da kasar Sin ta samar wa kasar Philippines ya isa birnin Manila, babban birnin kasar, wanda ya kasance allurai na farko da kasar ta samu tun bayan barkewar annobar. Sai dai a yayin da kasashe masu tasowa ke fama da matsalar karancin rigakafin, ita Amurka ta rika adana alluran da ta hada saboda manufar “fifikon kasar Amurka a kan sauran kasashen duniya” da ta aiwatar, matakin da ya bar dimbin rigakafin da dama suka lalace a banza, rigakafin da ka iya taimakawa wajen ceton dimbin rayukan al’umma.
Rahoton na Reuters ya jawo fushi daga bangarori daban daban. Mr. Harry Roque ya ce, idan Amurka ba ta son samar da rigakafinta ga Philippines, to, shi ke nan, amma me ya sa ta shafa kashin kaji ga rigakafin da sauran kasashe suka samar. A nata bangare, hukumar lafiya ta duniya WHO a martanin da ta yi, ta jaddada cewa, “rigakafin Sinovac yana da inganci, kuma yana iya magance nuna alamu masu tsanani, kai har mutuwa sakamakon cutar”. Hukumar ta kuma yi nuni da cewa, “Mai da rigakafi a matsayin makami na siyasa, zai iya haifar da mummunan sakamako.”
Abin hakan yake, yada karairayi zai iya haifar da babbar barazana ga lafiyar al’umma. Amma a zahiri dai, ba lafiyar al’umma ba ce ke jawo hankalin Amurka. Wani jami’in kasar Amurkan da ya sa hannu a aikin ya ce, “Ba ta fuskar mahangar lafiyar al’umma muke kallon batun ba, a’a, abin da ke jan hankalinmu shi ne ta yaya za mu jefa kasar Sin cikin halin kaka-nika-yi.” Rahoton na Reuters ya kara da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta aiwatar da wannan aiki shi ne, sabo da tana jin tsoron tasirin matakin kasar Sin na rarraba rigakafinta ga kasashen duniya. Wani jami’in kasar da yake da hannu a aikin ya ce, “Ba mu kyauta ba wajen rarraba rigakafinmu ga kawayenmu, saboda haka abin da kawai muka iya yi shi ne mu shafa wa rigakafin kasar Sin bakin fenti.”
A yayin da kasar Sin ke dada bunkasa, ita kuma Amurka ta yi kuskure har ta dauki kasar Sin a matsayin babbar abokiyar takarar ta ta farko, lamarin da ya sa ta dauki matakai na dakile kasar Sin daga dukkan fannoni, ciki har da fannin yada labarai. Ba kawai ta fannin rigakafin da kasar Sin ta samar ba, har ma da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da ma motocin lantarki da kasar ke samarwa, wadanda ke samun karbuwa daga kasa da kasa.
In mun dauki misalin Afirka, Sin da kasashen Afirka suna ta inganta hadin gwiwarsu tare da cimma gaggaruman nasarori. Amma Amurka wadda ta dade tana nuna fin karfi a duniya ba ta ji dadin hakan ba, don haka ma muke ta kara karanta rahotanni da ke da alaka da batun “sabon salon mulkin mallaka”, da “tarkon bashi”, da “barazana daga kasar Sin” a rahotannin da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke watsawa.
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya taba bayyanawa a fili cewa, “Muna karya da yaudara da sata…Mun kuma samar da darasi na koyar da wannan.” Sau tari hakikanan abubuwan da suka faru sun shaida cewa, dabarar Amurka ce ta yada karairayi ta kafofin sada zumunta, a yunkurinta na shafa wa wasu kasashe kashin kaji.
Sai dai shafa bakin fenti ga sauran kasashe ba zai “sake daga martabar Amurka” ba, illa ya shaida yadda take nuna fin karfi da ma rashin amana. Kasa mai girma irin Amurka, kamata ya yi ta yi abin da ya dace. Me zai hana ta mai da hankali wajen gudanar da ayyuka masu ma’ana, da za su amfani kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa, maimakon yada karairayi?
Jama’a, shawara a gare ku kuma ita ce, ku yi hankali a lokacin da ku ke karanta rahotannin da ke shafa wa kasar Sin bakin fenti. (Mai zane:Mustapha Bulama)