Sharhin Fim Din ‘Ashe Za Mu Ga Juna’

Ashe Za Mu Ga

Daga: Musa Ishak Muhammad.

 

Suna: Ashe Za Mu Ga Juna.

Labari: Jameel Nafsin.

Tsara labari: Jameel Nafsin.

Kamfani: Hanan Synergy Concept Ltd.

Shiryawa: Hannatu Bashir.

Bada Umarni: Sheikh Isa Alolo.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Salisu S. Fulani, Umar M. Sharif, El-Mu’az Muhammad, Sadik M. Adam, Abbas Sadik, Jamil Dan Masu Kudi, Hadiza Gabon, Hannatu Bashir, A’isha Salsa da sauransu.

Fim dinAshe Za Mu Ga Juna, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata baiwar Allah mai suna Nafisa(Hannatu Bashir), wadda ta fada a kogin soyayyar wani saurayi mai suna Yazeed (Umar M Sharif), wanda su ka hadu ta kafafen sada zumunta na zamani. Sai dai bayan ta je ta same shi ne sun hadu bayan ya shaida mata ya shigo garinsu, sai kuma labari ya chanja ga Nafisa bayan ya shaida mata cewa ai ya sace ta ne, kuma ba za ta bar gidansa ba har sai ya cika burin da ya ke da shi a kanta.

A daya bangaren kuma gidansu Nafisa a na chan a na faman nemanta, musamman lokacin da Alhaji (Ali Nuhu) ya dawo ya na tambayar matarsa Zainab (Hadiza Gabon) ina Nafisa ta shiga? Sai ta shaida masa cewa ai sun fita da Faruk (Salisu S. Fulani). Ita dai Nafisa ‘ya ce gurun yayan Alhaji, sai dai ta dawo gidan Alhaji da zama ne bayan rasuwar mahaifinta. Shi kuma Faruk Dan Alhaji ne wanda ya kamu da son Nafisa tun ranar da ta dawo gidansu. Sai dai ita kuma ta yi mugun tsanar shi. Koda ranar da su ka fita taren ma, ta yi amfani da shi ne don a barta ta fita.

Kwana daya, kwana biyu babu labarin Nafisa ko labarin inda take, wanda hakan ya matukar tayar da hankalin Alhaji. Domin kuwa har sakawa ya yi ‘yan sanda su kama Faruk, saboda zargin da shi a ka hada baki a ka sace Nafisa. Sai dai daga baya an sako shi bayan an tabbatar da ba shi da laifi. Abubuwa duk sun chakude a gidan Alhaji, musamman ga Faruk wanda shi ne su ka fita tare, wanda kuma daga fitar tasu ne ba a sake ganinta ba.

Cigiyar da a ka bada a kafafen ‘yada labarai da kuma alkawarin da a ka yi na bayar da kudade masu yawa ce ta taimaka wajen gano inda Nafisa ta ke, domin mai babur dinda ya kaita lokacin da ta je gidan saurayin nata Yazeed ne ya ga sanarwar da kuma hotonta. Sai ya zo ya shaida musu ya son gidan da ya kai ta, nan take kuwa Faruk su ka tafi da ‘ yan sanda, kuma su ka kwato ta, sannan a ka kama Yazeed da ya sace ta.

ABUBUWAN YABAWA

  1. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
  2. Fim din ya samu aiki mai kyau domin ba a samu matsalar sauti ko hoto ba.
  3. Jaruman fim dinsun yi kokarin isar da sakon da fim din ke dauke da shi.

KURAKURAI

  1. Ba a bayyana dalilin da ya sa Yazeed ya sace Nafisa ba, tun daga farkon fim dinhar karshe.
  2. Me ya sa Yazeed bai yi tunanin za a iya kama shi ba, tunda har gida Nafisa ta zo sannan ya tsare ta, ba ya tunanin wani ne ya kawo ta wanda idan ya ga bai ganta ba zai iya biyo sahunta har gidan.
  3. Me ne ne ribar Yazeed da ya saka shi ya sace Nafisa? Domin bai bayyana mata dalilin sace ta ba, alhalin tun farko ya fada mata cewa akwai dalilin da ya sa ya sace ta.
  4. Ba a bayyana hukuncin da a ka yi wa Yazeed ba sakamakon sace Nafisa da ya yi.
  5. ‘Yan sanda sun kama Faruk, amma ko sau daya ba a hasko a na binciken sa ba, kawai sai a ka ce wai an wanke shi. Ya kamata a ga ta yadda a ka bincike shi.

KARKAREWA

Fim din Ashe Za Mu Ga Juna, fim ne da ya zo da wani hardadden labari mai wuyar ganewa. Domin hakikanin sakon da a ke son isarwa bai bayanna ba har fim dinya kare. Sannan akwai abubuwan da a ka bar mai kallo a cikin duhu, kuma ba a fito da su ba har fim din ya kare.

 

Exit mobile version