Hamza Gambo Umar" />

Sharhin Fim Din ‘Furuci’

 

Suna: Furuci

Tsara Labari: Buhari Isa Dandume

Shiryawa: Nazir Dan Hajiya

Bada Umarni: Sadik N. Mafia

Jarumai: Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Tijjani Asase, Fati Washa, Hafsa Idris, Baballe Hayatu, Fatima Kebi, Teema Yola. D.S.S

Kamfani: Dan Hajiya Production

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Nuratu (Hafsa Idris) ta fito daga gida tana waya da mijinta Dakta Hamza (Ali Nuhu) bayan ta bude motar ta tashiga sai aka nuno an shake mata wuya an kashe ta. Jin ihun ta ne a waya ya fargar da mijin ta, nan take ya bazamo ya taho gida. Da zuwan sa kuwa ya tarar da gawar Nuratu a mota. Tunanin sa sai ya sauka akan abokin gabar gabar Nuratu wato Faris (Nuhu Abdullahi)wanda yake furucin zai kashe ta a sanadiyyar sun yi rigima da ita a makaranta an koreshi. Tunawa da hakan ne yasa jami’an tsaro suka cafke Faris suna tuhumar sa akan kashe Nuratu domin ya gama yadawa a gari cewa idan ya ganta sai ya kashe ta. Akwai wata budurwar Faris wadda ta kasance lauya Salma (fati washa) wadda ta samu labarin abin da ya faru da faris. Itace ta tsaya wajen ganin ta wanke shi daga zargin da ake yi masa. Ta soma bin diddigin abinda ya faru tana tambayar abokai da iyayen Nuratu don gano gaskiyar lamari, akan binciken da take yi ne ta gane cewa da sa hannun kishiyar nuratu a mutuwar ta wato Zaituna (Fatima Kebi) wadda ta bada kwangila aka kashe mata Nuratu saboda mijinta ya aure ta ba da sanin ta ba. Bayan an gano gaskiyar wanda yayi kisa ne jami’an tsaro suka wanke faris daga laifin da ake zargin sa dashi.

Abubuwan Birgewa:

1- An samar da labari mai karfi wanda ya bayyana illar da wasu mutanen ke ja wa kan su ta hanyar yin mummunan furuci.

3- Wakar fim din tayi dadi ba laifi

3- Jaruman sun yi kokari wajen isar da sakon labarin.

 

Kurakurai:

1- Kayan da jaruman suka saka a wajen waka irin na ‘yan kauye, da kuma kwalliyar da ‘yan matan sukayi sam basu dace da labarin fim din ba. Domin an nuna fim ne na birni ba na kauye ba.

2- Mai kallo bai ga lokacin da Salma ta karbi lambar mahaifin Faris a asibiti ba, amma sai aka ga ta kira sa ta hada shi da Faris sun yi magana a lokacin da tazo police station inda aka sanarwa da Faris mota ta buge mahaifin sa. Shin dama tana da lambar mahaifin faris din ne?

3- A lokacin da faris ya samu labarin cewa mahaifin sa yana asibiti mota ta buge shi, an nuna farar rigar jikin faris da jini, amma daga baya lokacin da Salma ta dawo take tambayar sa akan ya gaya mata gaskiya idan shi ya kashe Nuratu, a sannan rigar jikin sa fes take babu jini, shin wanke masa rigar aka yi?

4- Ya dace ace tun a farkon fim din an nunawa mai kallo cewa dakta Hamza matan sa biyu, bawai sai bayan labari yayi nisa za’a nuna hakan ba, wannan tamkar dawo da hankalin mai kallo baya ne.

5- Akwai lokacin da barista Salma taje wajen kawar Nuratu wato Muniba (teema yola), Salma tace wa Muniba dakta Hamza ne ya kwatanto mata gidan su, mai kallo yaji Salma ta ambaci gida amma sai aka gansu a zaune a wajen shakatawa. Shin Salma bata san bambancin gida da wajen shakatawa bane? Ko kuma dama tasan Muniba tana wajen shakatawar ne da har ta biyo ta?

6- Abin daukar sauti ya fito a cikin camera a lokacin da jami’an tsaro tare da Salma suka rutsa dan daban da ya kashe Nuratu.

7- Ya dace ace dakta Hamza ya dau mataki akan Faris ta hanyar mika shi ga jami’an tsaro tun kafin a kashe Nuratu, domin barazanar da faris yake yi tayi yawan da za’a ce an zuba masa idanu ba tare da an yi ‘karar sa ga hukuma ba.

8- Shin faris bashi da dangi ne sai mahaifin sa kadai? Ya dace ace an ga halin da dangin sa suke ciki a lokacin da iftila’i ya same sa. Kuma ya dace aga makomar mahaifin faris wanda mota ta buge aka kai shi asibiti.

 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar, amma akwai abubuwan da

Exit mobile version