Musa Ishak Muhham">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Khairiyya’

by Musa Ishak Muhham
October 1, 2019
in BIDIYO
3 min read
Sharhin Fim Din ‘Khairiyya’
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Suna: Khairiyya.

Tsara labari: Umar S. Umar.

Kamfani: ARIKYA Films Production.

Daukar Nauyi: Umar S. Umar.

Bada Umarni: Abdulhamid Abdulkadir.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Hadiza Muhammad, Alhassan Kwalli, Fatima Abubakar, Aminu Sharif, Ladi Muhammad, Hauwa Waraka, Nuhu Abdullahi, Zakiya Lawan, Fatima Makamashi da sauransu.

Fim din Khairiyya, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani mutumi Alhaji Bashir (Alhassan Kwalli) da kuma matarsa Hajiya Binta (Hadiza Muhammad), wadanda ‘yar aikin gidansu Mai suna Baraka( Fatima Makamashi) ta gudu da ‘yarsu tun ta na jaririya mai suna Khairiyya ( Fatima Abubakar). Sannan ta je kuma ta kai ta gidan Maman Bariki wato ( Ladi Muhammad). A cikin wannan gidan ne a ka raine ta har ta zama budurwa, wanda daga nan ne a ka fara shigar da ita cikin harkar karuwanci.

A farkon fim din an nuna su Khairiyya da sauran abokan harkokinta a bakin titi su na jiran sauran abokan harkokinsu su zo su dauke su. Su na nan tsaye a titi sai ga Alhaji Bashir ya zo zai wuce, kawai sai ya hangi Khairiyya, kawai sai ya ji ta birge shi, sai ya tsaya ya ce zai tafi da ita. A lokacin da su ka je gida shi ne ya ke tambayar ta labarinta. Shi ne ta ke fada masa cewa ita makaranta ma ta ke zuwa, amma saboda ba ta yadda yadda yadda yadda yadda yi shiyasa ta ke wannan muguwar dabi’ar. A nan ne Alhaji ya ke shaida mata cewa babu matsala shi daman dan ya taimake ta ya dakko ta. Kuma sannan ya na so ta maida hankali a kan karatunta, kuma a shirye ya ke ya bata kowacce iriyar gudunmawa da ta ke bukata.

A haka dai Alhaji ya yi ta taimakawa Khairiyya ta kowanne bangare, wanda hakan ne ya sa har ya fara tunanin dawo da ita gidansa domin ta ci-gaba da rayuwa a nan. Sai dai wannan yunkuri nasa ya gamu da tasgaro domin kuwa Hajiya Binta ba ta yarda da wannan tsarin ba, domin ta na tsoron kar Khairiyya ta zo ta kwace mata miji har gida. Saboda hakan ne ya sa Hajiya ta ringa bibiyar Khairiyya har makaranta domin ta yi mata gargadi a kan ta fita hanyar mijinta.

A karshe dai bayan dogon binciken da su Hajiya Binta su ka ringa yi, sun samu labarin Baraka, wadda ta ke basu hakurin laifin da ta yi mu su, kuma daga nan ne ta ke ba su labarin cewa ai Khairiyya ita ce ‘yarsu da ta gudu ita. Amma ta chanja mata suna ne saboda kar a gane ta. A karshe dai Khairiyya ta dawo wajen iyayenta na asali wato Alhaji Bashir da kuma Hajiya Binta.

1. Fim din ya dace da sunansa, domin duka labarin fim din ya na komawa ne ga ita Khairiyya.

2. Fim din ya samu aiki mai kyau, tun daga shiryawa har dauka.

3. Hotuna ma sun fita radau.

4. Sauti ma sai son barka.

5. Fim din ya nuna muhimmancin ceto rayuwar mutane daga mara kyau zuwa mai kyau domin kuwa su ‘ya’ya na kowa ne, kamar yadda Alhaji Bashir ya yi wa Khairiyya duk da cewa bai son ‘yarsa ba ce.

Kurakurai

1.Tsarin labarin bai tafi kai tsaye ba a cikin fim din.

2. Ya kamata ace Alhaji Bashir da Hajiya Binta sun shigo da hukuma cikin neman ‘yarsu tun farkon dauke ta.

3. Bai kamata a labarin a nuna Baraka ta mutu ba ta fadawa su Alhaji ina ‘yarsu ta ke ba.

Karkarewa

Fim din Khairiyya fim ne da ya yi nasarar isar da sako mai matukar muhimmanci ga masu kallo. Fim din ya samu aiki mai kyau da kuma labari mai kyau, hakan ne ya sa fim din bai samu matsaloli da yawa ba. Fatanmu dai a kodayaushe shi ne a inganta domin a samu nasarar gamsar da masu kallo.

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Sace Farfesa A Adamawa

Next Post

Inganta Rayuwar Al’umma Ta Hanyar Waka Shi Ne Babban Burina –Fatima Muhammad

RelatedPosts

Sharhin Fim Din ‘Uwa Biyu’

Sharhin Fim Din ‘Uwa Biyu’

by Musa Ishak Muhham
7 days ago
0

Daga: Musa Ishak Muhammad Suna: Uwa Biyu. Labari: Haidar M....

Corona Birus

Sharhin Fim Din ‘Corona Birus’

by Musa Ishak Muhham
3 weeks ago
0

Suna: Corona Birus. Tsara labari:  Nabil Salisu. Kamfani: Girma Multimedia...

Sharhin Fim Din ‘Gidan Na Rage’

Sharhin Fim Din ‘Gidan Na Rage’

by Musa Ishak Muhham
1 month ago
0

Suna: Gidan Na Rage. Tsara labari: Auwal M. Sarki. Kamfani:...

Next Post
Inganta Rayuwar Al’umma Ta Hanyar Waka Shi Ne Babban Burina –Fatima Muhammad

Inganta Rayuwar Al’umma Ta Hanyar Waka Shi Ne Babban Burina –Fatima Muhammad

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version