Hamza Gambo Umar" />

Sharhin Fim Din ‘Mayafin Sharri’

Suna: Mayafin Sharri

Tsara Labari: Hamza Gambo Umar

Kamfani: Media Suite Limited

Shiryawa: Sani Indomie

Umarni: Usaini Ali

Jarumai: Sani Garba S.K, Isyaku Jalingo, Sani Indomie, Yasira B. Yola, Zubaida Adam, Aisha Ahmad, Saliha Usaini da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Laure (Yasira B. Yola) ta tsaya a gefen bandaki ta na leke, yayin da makociyar ta Zainabu (Zubaida Adam) ta fito daga daki za ta zubar da shara ta tambayi Laure abinda take leke, jin hakan ne yasa Laure ta nuna mata cewar ta tsaya a wajen ne saboda ganin juna biyun makociyar ta Baraka ya tsufa tana jiran taji ihun ta sai ta kai mata dauki, jin hakan ne ya sa Zainabu ta nuna mata rashin dacewar hakan, yayin da Laure ta kasa fahimtar ta har su ka sami sabani.

Laure ta kasance mace mai tsegumin tsiya da rashin son zanan lafiya, hakan ne ya sa da ta je gidan wata kawarta Yalwa ta ga ‘yar mijinta zata fita unguwa ta nuna cewar a tuhumi yarinyar tana zargin ta da bin mazan banza kuma da alamun tana da juna biyu, a sannan ne mahaifin yarinyar wato Falalu (Sani Garba S.K) ya fito daga daki gami da tabbatar wa da matar sa Yalwa idan bata hana Laure shigowa gidan sa ba to zai debowa Lauren ‘yan sanda, ashe Laure ta labe taji duk maganganun su hakan yasa ta gudu daga gidan, sai dai kuma tun akan hanyar komawar ta gida taci karo da wata kawarta Habiba wadda take zawarci, yayin da Habiba ta tabbatar mata da cewar soyayya suke da Falalu mijin Yalwa. Jin hakan ne yasa Laure taci alwashin sanar da Yalwa cewar za’a yi mata kishiya da mace ‘yar bariki.

Kwatsam wata rana Baraka ta bar wa Laure suyar nama ta shiga bandaki, yayin da kamshi ya dami Yawale mijin Laure ya nuna lallai sai ta debo masa naman da aka bata ajiya, hakan yasa Laure ta kwashe soyayyan naman gaba daya ta maye gurbin sa da albasa akan wutar, ashe Zainabu taga duk abinda ke faruwa nan ta sanar da Baraka abinda Laure tayi yayin da Laure ta juye maganar ta nuna Zainabun ce ta kwashe mata nama ta zuba albasa, rigima har ta kai gaban Auwalu (Sani Indomie) mijin Zainabu wanda ya bawa Zainabu rashin gaskiya.

Wata rana Laure ta fadawa kawarta Yalwa cewar mijinta zai auro mata Habiba ‘yar duniya wadda ake zargin tana dauke da cutar kanjamau. Jin hakan ne ya tashi hankalin Yalwa suka soma rigima da mijinta Falalu wanda bayan ya gane cewar Laure ce ta sanar da matar sa abinda ke faruwa sai ta yaje ya gargadi Yawale mijin Laure akan baya son alakar da iyalan nasu suke, yayin da Yawale ya goyi da bayan matar sa Laure har hakan ta kai su ga sa’insa. Bayan Yawale ya dawo gida ya nunawa Laure rashin jin dadin sa akan rigimar da take jawo masa, sai ta fada masa dalilin faruwar abin duk akan Habiba ne. Jin hakan ne ya ruda Yawale ya bazama neman Habiba saboda shima yana kaunar ta, sai dai bayan ya je wajen Habiba ya bayyana mata soyayyar sa sai ta nuna an kusa auren ta da Falalu, jin hakan ne yasa Yawale ya hure mata kunne gami da nuna cewar shine yafi dacewa da ita. Hakan yasa suka soma soyayya wanda a karshe Falalu ya rutsa su har abin ya kai su ga dambe a tsakanin su. Kwatsam labari ya samu Laure cewar mijin ta zai auri Habiba. Hakan yasa taje tambayar Habiba dalilin da yasa zata auri mijin ta, amma bayan Habiba ta gaya mata sai Laure ta tabbatar mata da zata sa a saki Yalwa in har zata hakura da auren mijin ta, bayan sun yi yarjejeniya ne sai Laure taje ta zuba Yalwa akan irin munanan abubuwan da zata yiwa mijin ta don ya fasa auren Habiba, sai dai cikin rashin sa’a hakan ya jawo dalilin da aka saki Yalwa yayin da Habiba ta auri Falalu, ita kuma Yalwa suka raba hanya da Laure saboda sanin makircin da ta hada mata, wanda abin ya kai su ga dambe a karshe kuma Yawale mijin Laure ya nuna cewar ya gaji da halin ta don haka kawarta Yalwa zai aura. Duk da Laure ta nuna masa cewar ta yi nadamar halin ta amma hakan bai sa Yawale ya canja ra’ayin sa ba.

Abubuwan Birgewa:

  1. Sunan fim din ya dace da labarin, wato “Mayafin Sharri”.
  2. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa, domin har ya dire bai karye ba, kuma an yi kokari sosai wajen rika me kallo.

  3. Hoto ya fita radau.

  4. Darakan fim din yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace.

  5. Jaruman sun yi kokari domin sun taka rawar da ta dace, musamman Laure (Yasira B Yola) tayi kokari sosai wajen isar da sakon da ake bukata.

  6. An samar da wuraren da suka dace da labarin, wato “ locations “.

Kurakurai:

  1. An samu matsalar daukewar sauti na ‘yan sakwanni a wasu sassa na cikin fim din.
  2. A karshen fim din bayan Falalu (Sani Garba) ya saki matar sa Yalwa, me kallo yaji Yawale (Isyaku Jalingo) yace, “gobe za’a daura auren sa da Yalwa” Sai dai kuma ba’a nuna tazara ta dan wani lokaci ba a tsakanin sa’in da Falalu ya saki Yalwa da kuma lokacin da Yawale yayi wannan furucin na auren Yalwa, Shin Yawale bai san da cewa Yalwa sai tayi idda sannan zai samu damar auren ta bane, ko mancewa yayi da hakan bai fada ba? Ya dace ya furta cewar bayan Yalwa ta gama idda zai aure ta ba wai a sa’in da aka saketa din yace gobe zai aure ta ba.

3 Lokacin da Laure (Yasira B. Yola) ta kawo wa Yalwa magani a bakar leda, wanda sanadin sa ne aka saki Yalwa, me kallo yaga Laure ta jawo Yalwa da nufin fada mata wata magana a kunne, amma sai akaji ta rada wa Yalwa cewa “mijin ta zai mata duka har da saki” shin ya akayi Laure ta san hakan zai faru? Ya dace a cire sautin wajen saboda an nuna cewar sirri ne wanda ba’a son me kallo yaji.

  1. Kayan da Falalu ya saka (Sani Garba a lolacin da ya saki matar sa Yalwa, sune dai kayan da Yawale ya saka a jikin sa a lokacin da ya fara zuwa hira gidan su Habiba. Musamman idan aka kalli rigar Yawale wadda babu maballi (cufflinks) a jikin ta, haka shima Falalu gaban rigar ta sa babu maballi. Shin anko suka yi ne?
  2. Lokacin da Sagir (Abdul M. Sharrif) saurayin Hafsa ya tare Laure akan hanya don jin halayen budurwar da zai aura, me kallo yaji Laure ta tabbatar masa da cewar Hafsa fasika ce wadda har kwarto ta kawo cikin gidan su kuma silar hakan hakan yasa kwarton ya fasawa mahaifin Hafsa kan sa. Amma sai gashi bayan Sagir yaje gidan su Hafsa bai ga rauni a kan fuskar sa ba, matsayin Sagir na mai hankali ya dace yayi mamakin rashin ganin tabbacin abinda Laure ta fada masa kafin yayi yunkurin daukar matakin rabuwa da Hafsa. Idan kuma ana so a nuna tabbacin abinda Laure ta fada masa ne to ya dace a samar da rauni a gefen fuskar Falalu, tunda dama ance Yawale yayi masa rauni sa’in da sukayi rigima akan Habiba.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar, kuma ya fadakar, domin an yi kokari wajen nuna illar gulma gami da karshen halayen wasu munafukan matan masu haifar da husuma a cikin al’umma. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version