Sharhin Fim Xin ‘Akeela’

Daga: Musa Ishak Muhammad

Suna: Akeela.
Tsara labari: Jameel Nafseen.
Kamfani: Today’s Life Nigeria Limited.
Daukar Nauyi: Mansura Isah.
Shiryawa: Muhammad Danlasan.

Bada Umarni: Sheikh Isa Alolo.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Sani Musa Danja, Yakubu

Muhammad, Salisu S. Fulani, Auwal Isa West, Baba Karami, Sultan Sani Danja, Fatima Shu’uma, Hannatu Bashir, Saratu Gidado Daso, Iman Sani Danja, Bilkisu Abdullahi da sauransu.

Fim din Akeela fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu ma’aurata biyu wato Sani(Sani Musa Danja) da kuma matarsa Fateema (Fati Shu’uma).

Su dai Sani da Fateema sun yi aure ne cikin farin ciki, kuma sun zauna cikin kaunar juna na tsahon shekara 10.

A tsahon wannan shekaru Allah Ya azurta su da samun ‘ya’ya guda biyu. Wato Muhsin (Sultan Sani Musa Danja) da kuma Akeela ( Iman Sani Musa Danja).

Sai dai wannan ‘ya’ya nasu ko kadan ba sa samun kulawarsu. Domin dukkanunsu tafiya su ke sabgoginsu su rabu da yaran a gida.

Duk da Sani ya na da kudi sosai, amma kulawa da iyalensa shi ne abunda ba ya iyawa.

Saboda wasu lokutan shi ya fita shakatawarsa a yawan dare, ita ma ta fice ta tafi nata sabgogin. Haka yaran za su zauna su kwana cikin gidan su kadai. Babu ruwansu da abincinsu ko abun shansu.

Sun fifita yawan barikinsu sama da ‘ya’yansu. A kodayaushe abokin Sani wato Jabir(Yakubu Muhammad) ya na yawan ba shi shawara a kodayaushe a kan ya maida hankali wajen kula da iyalensa, amma ko kadan ba ya jin shawararsa.

Haka dai Akeela da Muhsin su ka yi ta rayuwa cikin kunchi da kadaici. Ga su ‘ya’ya masu gata amma ko kadan ba sa samun lokacin iyayensu.

Ita Akeela ita ce ta ke ci-gaba da kulawa da kaninita. Ta shirya shi su tafi makaranta, kuma ta ke kulawa da dukkan damuwarsa. Wata rana sun dawo daga makaranta su na jin yunwa kuma babu abinci ko kadan a gidan, gashi Muhsin sai kuka ya ke a kan jin yunwa.

Hakan ne ya sa Akeela ta ce bari ta je ta gwada dafa musu abinci, wanda hakan ya sa ta kone a hannunta.

Watarana ma sun dawo daga makaranta ba abinci, sai su ka yanke shawarar su koma makaranta ko za su samu abincin da za su ci.

Bayan sun tafi ne sai Muhsin ya ga wata ledar biredi a jefe a gefen titi, ai kuwa sai kawai ya dauka ya kama ci.

Ya na cikin ci ne kawai sai ya fadi. Akeela ta na ganin shi a kwance, ta zo da gudu ta dauke shi ta tafi da shi asibiti.

Kuma ta tafi ta na roko domin ta samo kudin da za a yi wa Muhsin magani. A garin neman taimakon ne ita ma mota ta kade ta. Karshe dai Akeela da Muhsin duk sun rasa ransu sakamakon sakacin iyayensu.

Abubuwan Yabawa
1. Fim din ya samu aiki mai kyau.
2. An samu sauti mai kyau tun daga farkon fim din har zuwa karshensa.
3. Hotuna sun dauku sosai, ba a samu matsalar na’ura ba a cikin fim din.
4. Labarin fim din ya tsaru,domin bai yanke ba tun daga farko har karshe.
5. Sunan fim din ya dace da labarin.
6. Fim din ya nuna muhimmanci kulawar iyaye ga ‘ya’yansu.

Kurakurai

  1. Sunan Akeela ya yi girma a matsayin sunan fim din. Saboda iya rawar da ta taka a cikin fim din bai kai a ce har sunanta ya koma sunan fim din ba.
  2. Lokacin da Muhsin ya fadi a lokacin da ya ke cin biredi, kamata ya yi ace wani abu ya ci mai nau’in guba ba wai kwalba ba. Domin girmansa ya wuce ya ci kwalba bai sani ba. Kuma girman kwalbar da Akeela ta d’aga ba zai yi wu a yi hadiye ta cikin rashin sani ba.

KARKAREWA

Fim din Akeela ya samu aiki mai kyau. Kuma ya samu nasarar isar da muhimmin sako a cikinsa. Fim din ya na daya daga cikin fina-finan da su ka samu haskaka a cikin shekarar da ta gabata ta 2019.

Exit mobile version