Dr. Auwal Ado Aujara" />

Sharhin Littafin ‘Ilimin Rubutun Labari Cikin Adabi (Turbar Addini Da Al’ada)’

Sunan Littafi: Ilimin Rubutun Labari Cikin Adabi (Turbar Addini Da Al’ada)
Kamfanin Bugu: Garba Muhammad Bookshop
Marubuci: Hashim Abdallah
Yawan Shafuka: 131

Marubucin Littafin
Malam Hashim Abdallah Tanko ya kasance mutum mai hazaka da kaifin basira a lokacin da na san shi yana dalibi. Ya kara tabbatar min da kwazonsa bayan ya kammala karatu a kwalejinmu,
Bayan da ya yi yunkurin ci gaba da karatu har shigarsa jami’a, yana tuntuba ta kan al’amura da yawa musamman abin da ya shafi ilimin adabi da harshen Hausa. Saboda haka, ban yi mamaki ba a lokacin day a kawo min wannan littafi na duba bayan ya rubuta shi. Da na karanta littafin na sami cikakken yakini a cikin zuciyata cewa daya daga cikin bishiyar da muka dasa ta kantsama ‘ya’ya masu dadi da za a dade ana amfana. Kuma ya kasance wata korama ta ruwan ilimi da muke fata za ta dade tana gudana domin samun ruwan da za mu ci gaba da shayar da sauran shukoki.
Za a lura da cewa, dangane da wannan littafi mai suna “Ilimin Rubutu Labari Cikin Adabi: Turbar Addini da Al’ada” na kalli abubuwa guda uku ne kacal: manufar littafin da yadda zubi da tsarinsa yake, da kuma salon isar da sako da irin yadda marubucin ya yi amfani da harshensa. Wadansu abubuwa uku a fagen nazari su aka fi maida hankali a kansu, domin su ne suke fito da basirar marubuci.
Ina matukar nuna godiyata ga marubucin wannan littafin saboda damr day a ba ni da kuma karramani da yayi wajen zabo ni a matsayin wanda zai yi bitar wannan littafi, hakan bakaramar dama bace agareni ba.
*Muhimmancin littafi: fadakarwa da ilimantarwa da shawara ga marubuta labarai da fina-finai. Ba gare su ba kawai, har ma da dalibai da masu nazari ko bincike a fagen adabi.
*Gyara dabi’u da saita tunanin marubuta da masu shirya fim.

Sharhin Littafin
Wannan littafi mai suna ‘Ilimin rubutun Labari Cikin Adabi: TurbarAddini Da Al’ada’ ya kunshi babi har gud 11 cikin shafuka 131. Abubuwa guda uku ne kacal a littafin:
1. ManufarLittafin.
2. Zubi da tsarinLittafi
3. Salon isar da sasako da irin harshen da marubucin yayi amfani wajen cimma burin wadannan abubuwa uku a fagen nazari su aka fi mai da hankali a kansu domin su ne suke fito da basira da kuma kwarewar marubuci.
Idan mun duba, tun daga sunan littafin za za mu fahimci abin da masu nazarin kagaggun labara suke cewa: ‘Jigo Jimla’.
Akwai al’ada da addini da kuma adabi. Al’ada itace hanyar gudanar da rayuwar al’umma ta yau da kullum; wadda ta hada da tsarin abinci da tufafi da muhalli da mu’amala kowace iri da sauransu. Addini kuma shi yake daidaita rayuwar al’umma tsakaninsu da mahalicci (Allah) da kuma mu’amala a tsakanin junansu. Shi kuwa adabi madubin rayuwar al’umma ne da yake fito da yadda suke gudanar da rayuwarsu.
Don haka a takaice wannan littafi an tsara shi ne don saita madubin da za mu kalli yadda al’umma take gudanar da rayuwa. Kenan littafin fitila ce da ke haska hanya ga duk wani mai son ya nuna yadda rayuwar Hausawa take don ya bi ta dodar babu gargada, ko batan kai.
Babi na daya: Ya kunshi tarihin kagaggun labarai da kuma dalilan da suke sa wa a rututa kagaggun labarai a wannan zamanin; tarihin kagaggun labarai (tushensu ita ce tatsuniya)
*Dalilai da kesa a rubuta labarai musamman a wannan zamani, kamar nishadantarwa da fadakarwa da mayar da martani da sauransu.
Babi na biyu: Ya kawo ma’anar adabi da rabe-rabensa. Gibin rubuce-rubucen matasan Hausawa wajen isar da sako da ya dace da ala’dun Hausawa da tunaninsu. Ya kawo jerin abubuwa da rubutun kagaggun rabarai ko fim ya kamata ya kalla wanda ya dace da al’adu da addini da sana’oi da muhalli da tarihi da makamantansu. Da abubuwa kamar:
*Dangantaka da banbancin rubutaccen adabi da adabin baka/ka
*Samuwar rubutaccen adabi bayan zuwan Musulunci da Kirista(Turawa)
*Ya rarraba adabi zuwa, kashi hudu: 1. Waka 2. Zube, Wasan Kwaikwayo 4. Fim.
*Tushen samuwar fim din Hausa daga rubutattun kagaggun labarai
*Ya kawo jerin abubuwa da rubutun kagaggen labari ko fim ya kamata ya kalla; al’ada da addini da harshe da sana’a da muhalli da tarihi.
Babi na uku: Ya yi bayanin waye ma marubucin kagaggen labari, sannan ya kawo hanyoyin da za a bi a zama marubuci har guda 13. Misali, neman ilimi da tunani mai zurfi da lura da abinda yake faruwa da mafarki da sauransu.
*Babi na hudu: Ya kawo tubalan ginin rubutun zube, wadanda kuma su ne mai nazari yake bibiya koyaushe.
*Babi na biyar: Ya kawo hanyoyi da mutum zai bi ya kware wajen rubutu. Domin sakonsa ya isa ga jama’a da kuma shawarwarin yadda za a fadada manufofin labarai a yau. Shawarwari yadda za’a fadada manufofi na labari su zarce na soyayya da aure da sarauta cikin rubuce-rubuce na kagaggun labarai da fina-finan Hausa.
*Babi na shida: Ya fito da wasu matsaloli da marubuta suke fuskanta, rashin sanin kalmomin Hausa, da kuma musamman kasa kiyayewa da bin ka’idojin rubutu da kuma satar fasaha da kasa kiyaye ka’idojin rubutu. Yadda ya kamata a tunkari fassara da aron fasaha.
*Babi na bakwai:- ya fito da wasu abubuwa da marubuci zai lura da suka shafi al’umarsa, musanman al’amuran addini da kyawawan al’adu da koyar da tarbiyya; kamar dai kaucewa batsa, bakin al’adu da sauransu.
*Babi na takwas: Ya yi bayanin tunanin al’umma da hukumomi da salon rubuce-rubuce da ake yi da kuma fina-finan Hausa. Ya ja hankalinsu kan matakan da ya dace su dauka domin inganta harkar, musamman rawar da malaman addini da masana adabi ya kamata suke takawa wajen inganta sana’ar.
*Babi na tara: Ya kunshi rawar da jarumai ko taurari ya dace su taka daidai da yadda aka bukace su. Kuma ya kawo wasu shawarwari ga jarumai ta yadda za su zama kwararru. Horar da jarumai da matsayin da suka dace su fito da samar da nishadi da sauransu.
*Babi na goma: ya yi bayani yadda za a gyara harkar rubutu da fina-finai ta hanyar ba da shawara da nuna kura-kurai da gyara ko kuma yabawa a inda aka yi rawar-gani.
*Babi na goma sha daya: Ya kawo wasu batutuwa da shawarwari da ya dace marubuta su rika tabowa.
Gabadaya kunshiyar littafin ta taskace bayanai game da ilimin rubutu da hanyoyin da za a samar da kagaggun labarai da fina-finai da suka dace da al’adunmu wadanda suke tafiya kan doron shari’a, da kuma kaucewa munanan dabi’u da sakarci da, watakila, ke faruwa. Sannan ya kawo shawarwari yadda za a samarwa rubuce-rubucen kagaggun labarai da fina-finai karbuwa a wajen al’umma.
Ba wai kawai al’adu ake kalla ba, marubutan kagaggun labarai da masushirya fina-finai suna taka muhimmiyar rawa wajen isar da sakonni na addini, wanda cikin dan kankanin lokaci yake isa ga jama’a. Misali, littafin Ruwan Bagaja na Alh. Abubakar Imam ya nuna illar jahilci lokacin da Mallam Zurke ya je cikin jahilai. Fim din Ahalul Kitabi na Adam A. Zango ya isar da wani wa’azi ga mabiya addinin Kirista, domin na ji Adam A. Zango yana cewa mutum uku ne wai suka Musulunta sanadiyyar sakonnin cikin fim din.
Don haka littafin yana da muhimmanci don ya kunshi fadakarwa da ilimintarwa da shawarwari ga marubuta labarai da suke hangen abubuwan daga nesa. Haka littafin zai taimakawa masu sha’awar zama marubuta ko shirya fina-finai. Sannan zai taimaka wajen saita tunanin maruba ko shirya fina-finai da kuma gyara dabi’unsa.
Hakika wannan littafi ya amsa sunansa domin an rubuta shi bisa binkice da nazarin wasu littafai da mujallu da su ka danganci adabi da al’adun Hausawa, har da ma wasu fina-finai da aka kalla.
*Masu iya magana sun ce hannun marubuci makaho ne, don haka, ba za a rasa kura-kurai ba.

Dr. Aujara ya rubuto, Jigawa State College of Islamic and Legal Studies Ringim, Jigawa State.

Exit mobile version