Alkalin kotun shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano, Abdullahi Halliru, ya umarci ‘yan jirida da su fice daga kotun domin Asiya-Balaraba Ganduje wato diya ga gwaman jihar, Ganduje, ta gabatar da takardar karar kashe aurenta da ta shafe shekara 16 da mijinta Inuwa Uba.
Ko da ya ke, alkalin ya ce, kowane mutum dai-dai ya ke da kowa a idon doka, inda ya kara da cewa, wannan karar ta musamman ce, wadda ba sai an wallafa ta ba, ganin irin mutanen da ke a cikin shari’ar.
- Wasu Mutane Sun Kashe Wata Mata Sun Cefanar Da Sassan Jikinta A Jihar Ogun
- 2023: ‘Yan Damfara Sun Bude Manhajar Intanet Don Daukar Ma’aikatan Zabe – INEC
Ya ce, zai yin wannan shari’ar ne a ofishinsa.
An ruwaito cewa, Balaraba ta bukaci kutun da ta raba aurenta bukatar bisa tsarin khul’i, kamar yadda shari’ar addinin musulunci ya tanada.
Mai sharia’a Khadi da ya yi dubi akan takadar karar, ya baiwa mijin wa’adin mako biyu da ya lalubo da hanyoyin da zai dai-dai da matarsa.
Khadin ya kuma kebe ranar 5 ga watan janairun 2023 domin ya yanke hukunci akan karar.
Sai dai, mijin Inuwa ya dage kai da fata cewa, har yanzu yana son matarsa tare da kuma bukatar kotun ta kara masa lokaci don ya samu ya shawo kan Balaraba.
An ruwaito cewa, a wasu shekarun baya, Balaraba ta samu sabani da mahaifanta saboda da koma wa bangaren mijinta wanda suka zarga da yin amfani da su don samun dukiyarsu.
Bugu da kari, an ruwaito wata majiya ta ce, bayan da Balaraba ta jure wa matsin da ta sha daga gun iyayenta ta kuma yi watsi da Inuwa, an tura jami’an tsaro zuwa gidan ma’auratan da ke a rukunin gidaje na Technical Staff, inda suka yi awon gaba da wasu takardun Ikadarorin Inuwa.
A cewar majiyar, kadarorin sun hada da na kan titin Kano zuwa Zaria da kuma takardun wasu gidajen sayar da man fetur da kuma wani gida da ke Abuja.