Daga Jamil Gulma
Sheikh Abubakar Giro ya yi kira ga iyaye da su bayarda cikakkiyar kulawa ga ilmin yayansu. Ya yi wannan kiran ne a garin Argungu jiya litinin sa’ilinda ya ke zantawa da wakilinmu.
Shehin malamin ya bayyana ilmi a matsayin ginshikin cigaban kowace al’umma saboda haka ya kamata kowane mahaifi ya tabbatarda samarda ingataccen ilmi ga yayansa tare da lura da irin abokan da su ke hulda da su saboda mafi yawancin dabi’u ana daukar su ne ta hanyar ma’amala, a duk lokacin da ka ga wata dabi’a wacce ba ka aminta da ita ba wajen yaranka ba to ka tashi tsaye sai ka tabbatarda ka kawarda ita wannan shi ne zama lafiya ga kowane mahaifi.
Shiryarwa kamar yadda Al’kur’ani ya tabbatar ba hannun kowa ta ke ba face Allah amma dai a matsayin ka na mahaifi ana so ne ka sauke nauyinda ke wuyanka na kowonda aka danka hannunka.
Ya kuma yi kira ga malamai da su kuma su ji taoro Allah wajen kiyaye amanar da aka danka hannusu da su rike dalibansu tamkar ’ya’yansu.