Yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin masu kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wato Glazers family da kuma masu son sayen kungiyar Sir Jim Ractliffe da kuma hamshakin dan kasuwa na kasar Qatar Sheik Jassim bn Hamad Al Thani.
Manchester United na gab da komawa hannun Sheikh Jassim bayan da ya ke gaba a wajen taya kungiyar da kudi masu yawa.
- Yadda Matar Shugaban DSS Ta Yi Barazanar Hana Ni Zama Gwamnan Kano –Abba Gida-Gida
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Wani Sabon Hari A Kogi
A baya an ta rade-radin cewar masu kungiyar Manchester United, Glazers sun samu rarrabuwar kawuna a tsakaninsu, inda daga cikinsu Abram da Joel Glazer suka nuna kin amincewarsu na sayar da kungiyar.
Sai dai yanzu komai ya dawo daidai kuma sun yarda a sayar da kungiyar matukar an samu wanda zai saye ta da daraja.
Yanzu haka dai magoya bayan Manchester United ba su da tabbacin wanda zai jagoranci kungiyar a badi yayin da kungiyar ta ke kasuwa a halin yanzu.
Manyan yan kasuwa Sir Jim Ractliffe wanda kuma shine mamallakin kungiyar OGC Nice ta kasar Faransa da kuma Sheikh Jassim bn Hamad Al Thani na kasar Qatar ne kan gaba wajen taya kungiyar da ke Greater Manchester.
Ana bukatar duk wanda ya samu damar sayen Manchester United zai shiga kasuwa domin zakulo sabbin ‘yan wasan da za su tunkari gasar badi ganin cewar Man Utd ta samu damar buga gasar Zakarun Turai.