Shekaru ashirin ba karamin abu ba ne a rayuwar mutum haka nan ma ba karamin abu ba ne a rayuwar kamfani. Abin ya fi a rayuwar jarida musamman a wajen da durkushewar jaridu ya zama abu mafi sauki fiye da kafuwarsu a wannan zamani.
Jaridu da dama da aka kafa a ‘yan shekarun da suka gabata duk sun mutu basu iya ko kai labari ba ma. Cikin abubuwan da suke kashe gidajen jarida da sauri sun hada da rashin talla daga abokan hulda, da kuma rashin sanya hannu gwamnati a harkokin jaridar ta hanyar ba jaridar kwangila.
- Kasar Sin Ta Kakaba Takunkumai Kan Wasu Kamfanonin Amurka 3 Da Manyan Jami’ansu 10 Don Gane Da Batun Sayarwa Yankin Taiwan Makamai
- Zan Yi Sanadin Ficewar Sakataren Gwamnatin Kano Daga NNPP – Hajiya Lami
Tsayuwar Jaridar LEADERSHIP kyam a kowane irin hali data samu kanta na nuni ga irin kokarin wanda ya kafa kamfanin, wato Sam Nda-Isiah, mutum wanda yake da hangen nesa, fafdandar zuciya, ga kuma dagiya a kan abin da ya yi Imani da shi a kai, da kuma zuciya ta rashin tsoro.
Karin maganar Turanci da ke cewa, “Oaks from little acorns grow” ya yi daidai da yadda jaridar da ta fara daga waje mai matukar karfafawa. Tana nan a cikin kwaryar Abuja kuma ta zama jarida mai matukar tasiri a harkar jaridu ba kawai a Nieriya ba har ma a fadin yankin Afirka gaba daya.
Bata faro a matsayin jaridar kullum ba. Ci gaban da aka samu ne ta hanyar LEADERSHIP Confidential ya haifar mata da wannan gaggarumar jaridar da muke kallo a yau.
Wani abu da ya fita daban game da jaridar da wanda ya samar da ita shi ne, basu da wata alaka ta aiki amma a haka suka hadu suka samar da wannan jaridar da ta yi karko.
Banda zaman mahaifinsa dan jarida da kuma zamansa editan karamar jarida a jami’a wato Pharmacists’ Journal, wata babbar daukaka ta kawo shi harkar jarida ita ce makalar da yake rubutawa a jarida wato “Last Word da kuma Earshot”
Lokacin da ya shirya tsaf domin tattara rubuce-rubucen shi zuwa littafi wanda ya sa wa suna; Nigeria: Full Disclosure: Selected Writings on Gobernance, Democracy and Statecraft, May 1999 – March 2004, Sam, kamar yadda ake kiransa da ya samu kimanin Naira Miliyan ashirin wadda ta zama jarin da aka kafa shi kamfanin jaridar da ita.
Kamar yadda aka saba, Jaridar LEADERSHIP ta gamu da kalubale da dama wadanda suka bude hanyar zuwa ga ci gaban da jaridar ta samu zuwa yanzu. Abinda yafi daukar hankali shi ne rasuwar wanda ya samar da jaridar, Sam, a ranar 11 ga watan Disamba, 2022. Ga shi kuma har yanzu jaridar tana nan tsaye saboda kokarin masu ba kamfanin shawara, masu gudanarwa da kuma ma’aikatan kamfanin wadanda suka yi koyi da tsayin dakan wanda ya samar da kamfanin.
Marigayi Sam Nda-Isiaah mutum ne mai ra’ayoyi. Yana yawan gwada su. Duk da ya karanci fannin bayar da magani ne, ya kasance rikakken dan kasuwa. Ya shiga harkokin kasuwanci da dama. Daga harkar noma, tsaro da kuma bangaren kimiyya da fasaha. Duk wannan ya yi su ne bayan gajeren aikin da ya yi da kamfanin magani na Pfizer.
Wasu daga cikin magoya bayan shi basu yarda da tunanin shi ya shiga siyasa ba. Amma shi mutum ne da baya tsoron kalubale yana kara kaimi wajen fuskantar duk abin da ya sa a gabansa.
Wannan lokaci ne ya gwada karfin tubalin ginin kamafanin da marigayi Sam Nda-Isiaah ya samar kuma haka ya tsaya kyam. Jaridar ta nuna cewa ta yi kwarin da za ta iya jure duk wani duk wani kalubale musamman daga abokan hamayyar siyasa wadanda suke son a hukunta shi domin yana so a kawo sauyi.
Lokacin da ya dawo daga harkar siyasar, ya tarar da Jaridar ta sha wahala amma bata rusuna ba. Tare da sauran ma’aikata suka hada hannu suka gyara jaridar ta dawo inda ya kamata ta zama a koda yaushe.
Abubuwan alkhairin sa sun ci gaba kamar yana raye. Hakan ya faru ne saboda ya tafi ya bar mutane wadanda suka yarda da shi kuma suna nan sun yarda da shi, bugu da kari kuma a shirye suke su ci gaba daga inda ya tsaya, karkashin jagorancin shugabar kungiyar, matar shi kuma wacce ta gaje shi wato Zainab Nda-Isiaah.
Bayan shekaru ashirin da samar da jaridar kuma shekara hudu bayan rasuwar wanda ya samar da jaridar, LEADERSHIP ta ci gaba da habaka, da taimakon masu karantawa, masu ba da talla, da kuma masu taimakawa a kai a kai.
Jaridar da tafi kowace tasiri tana nan tsaye domin yi wa Ubangiji da kuma kasa aiki.