Ranar 29 Ga Watan Oktoba ta wannan shekara ta 2026, Shekaru Ashirin cif da Nijeriya ta yi rashin wani nagartaccen da, mai son al’ummarsa da ci gaba tare da zaman lafiya watau Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido wanda shi ne Sarkin Musulmi na 19 a jerin wadanda suka yi sarautar tun daga Muhammadu Bello zuwa yanzu.
An haife shi a shekarar 1926 a Garin Dange da ke wajen Babban Birnin Jihar Sakkwato ga Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku (wanda ya yi sarautar na tsawon shekaru hamsin) da Uwargidansa mai suna Hauwa’u.
Tun yana karami ya taso da halaye masu kyau da kuma mamaki saboda shi baya bayyana cewa shi daga wani muhimmin gida ya fito wannan ya sanya lokacin da zai shiga Kwalejin Nagarta da ke cikin Birnin Sakkwato da aka tambaye shi sunansa ya fada wa Bature sunana Muhammadu Maccido. A haka ya kasance a kwalejin ba wanda yasan wani abu dangane dashi sai ranar da Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku Ya ziyarci kwalejin a lokacin da yake ziyartar makarantu domin ya ganarwa idanunsa irin wainar da ake toyawa, to, a wannan ranar ne dalibbai da malamai suka san cewa shi dan Sarkin Musulmi ne. Ya kuma yi karatu a mashahuriyyar kwalejin nan da ke birnin ilimi watau Kwalejin Barewa da ke Zariya daga nan kuma ya wuce Kwalejin South Debon da ke Birnin Landan a tsakanin shekarun (1952-1953).
Ya bayar da gudumuwa ga kasarsa Nijeriya ta hanyar ayyukan da ya yi wadanda suka kara daga martabar kasar a fannoni daban-daban, saboda saukin kansa da girmama kowa ba tare da kulawa da matsayinsa ba, ya sanya a shekarar 1951 aka zabe shi domin ya wakilci Lardin Sakkwato a Majalisar Dokoki da ke Kaduna, duk kuwa da karancin shekaru tare da kyakyawar tarbiya da kuma baiwa da Allah ya yi masa wadannan suka sanya shi samun girma da kuma daukaka a wajen shugabanni da ke jagorancin kasar wadanda ya yi aiki da su a majalisar.
Saboda irin muhimmiyar rawar da gogewarsa ya sanya shi rike mukamai Kansila a wurare uku kamar haka: Ya zama Kansilan Ayyuka a shekarar 1956, Kansilan Bunkasa Karkara a shekarar 1959, ya kuma zama Kansilan Ayyukan Gona a shekarar 1960. Haka kuma nagartattun halayensa da jarumtakarsa ya sanya aka tura shi a yankin Zamfara domin ya kwantar da kowacce irin barazana tare da samar da yanayi mai dauke da zaman lafiya domin a samu nasarar gabatar da zaben da aka yi cikin shekarar 1959 cikin lumana.
A lokacin da aka yi wani mummunan rikici bayan juyin mulkin da sojojin Nijeriya suka yi wanda ya yi sanadiyar kashe manyan shugabannin Arewa cikin kuwa har da Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, wasu fusatattun matasa a lokacin sun yi barazanar kona ginin Babban Chocin Katolika da ke Sakkwato, shi da Alhaji Umaru Shinkafi, Marafan Sakkwato wanda kuma Surukin Sardauna Ahmadu Bello ne, suka shiga tsakani ta hanyar tausaya da zancen kwantar da hankali, a karshen matasan suka kama gaban su ba tare da kona ginin chocin ba, su biyu suka yi kokarin ganin ba a zubar da jini ba.
Ya taba rike mukamin Kwamishinan Gona da kuma Kiwon Lafiya a Majalisar Zartasawa ta Arewa Maso Yamma. A Jamhuriyya Ta Biyu kuwa a tsakanin shekarun (1979-1983) ya rike mukamin Babban Jami’in Hulda tsakanin Masarautar Sakkwato da kuma Shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Ya kuma taba zama Shugaban Jam’iyyar NPN a lokacin kuma yana rike da sarautar “Sarkin Kudu” inda ya yi amfani da farin jininsa da iya zancensa wajen ganin Jam’iyyar NPN ta samu galaba a Babban Zaben da ya kawo Shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da Alhaji Shehu Kangiwa ga jagorancin Nijeriya da kuma Jihar Sakkwato. A shekarar 1986 ya bar siyasa domin mayar da hankalinsa kacokam ga kula da mahaifinsa da bashi da lafiya. A lokacin da Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku ya rasu a ranar daya Ga Watan Nuwamba na shekarar 1988. Yana cikin wadanda ke tafiyar ayyukan da suka shafi mulki a Masarautar Sakkwato.
A shekarar 1996 lokacin da Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya tumbuke Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki, sai aka ambaci sunansa a matsayin sabon Sarkin Musulmi. An kuma nada shi a Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke kusa da Fadar Sarkin Musulmi a ranar 21 Ga Watan Afirilu na shekarar 1996.
Wannan matsayin da Allah ya bashi ya sanya shi kasancewa Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya kuma Shugaban Majalisar Masarautar Sarkin Musulmi a Sakkwato. Yayin da Shehu Barno yake matsayin mataimakinsa haka wadannan mukaman su ke har a yau. Dubun dubatan mutane daga kowanne sashe na duniya suka yi wa Birnin Sakkwato tsinke domin halatar bukin nadinsa.
Allah ya bashi ikon jagorancin wannan mashahuriyyar fada har na tsawon shekaru goma, ga kuma wasu daga cikin nasarorin da ya samar a lokacinsa:
Sunan da aka fi saninsa dashi a kasar Nijeriya da Duniya shi ne Jigon Zaman Lafiya: Wannan ya tabbata a fili ganin irin muhimmiyar rawar da ya taka a cikin kasar musamman ta amfani da iliminsa da kuma kwarewar da ya samu a zumuncinsa da na gabansa a wuraren da ya yi aiki can baya da taimakon Allah ya dinke hular rikicin Tibi da Jukunawa a Jihar Taraba. Hasalima kokarinsa wajen ganin an samar da bakin rikicin kabilanci da na addini a yankin Arewancin Nijeriya ta hanyar hada hannu da Rabaran Fr. Mbah ya haifar da kirkiro da Hukumar Shiga Tsakani tare samar da zaman lafiya ta Addini a Nijeriya.
Bunkasa Kiwon Lafiya: A shekarar 2000 lokacin da mutanen Arewancin Nijeriya suka kauracewa Allurar Rigakafin da ake yi wa kanannan yara da mata masu juna biyu, Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido bai zauna ba, ya yi amfani da matsayinsa wajen shirya taro da sarakunan yankin inda ya wayewar da kawunan su dangane illar hakan ya kuma nemi su da su wayar da kawunan mutanen su domin ganin sun dawo rakiyar tunanin su, suka rungumi shirin da muhimmanci domin kaucewa illolin da hakan zai janyo daga baya. Wannan kyakkyawan mataki da ya dauka ya ceto rayuwar miliyoyin yara da iyayen su mata.
Bunkasa Ilimi: Ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ilimin Muhammadiyya da na Zamani sun bunkasa, ya kuma ba da gudumuwa kwarai wajen Ilimin Mata Musulmi a Nijeriya, ya samar da mashahuriyyar Makarantar (wadda aka sanyawa sunansa) domin koyar da Karatun Kur’ani da wasu Kwasakwasai a Birnin Sakkwato ta hanyar samun tallafin kudi daga kasar Saudiyya da wasu kasashen duniya domin ganin Sakkwato ta ci gaba da kasancewa cibiyar bunkasa ilimin Muhammadiyya a duniya. Ya kuma bayar da gudumuwa domin domin ganin masana tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen kyakkyawan bincike a kan Tarihin Daular Usmaniyya.
Bunkasa Ayyukan Gona da Tattalin Arziki: kwarewarsa a fannin ayyukan gona a matsayinsa na Kwamishinan Gona ya bashi damar gano muhimmancin daukaka martabar hukumomin bunkasa ayyukan noma da ke cikin Arewancin Nijeriya saboda su taimaka wajen ciyar da yankin da abinci ta amfani da fitowa da manyan filayen domin noma domin bunkasa tattalin arzkin yankin da kuma samar da wadatuwar abinci ga dimbin mutanen da ke yankin, domin kaucewa yunwa tare da matsalolin da za su haifar da rashin tsaro a tsakanin al’ummarsa.
A shekarar 2004 ya dagawa kansa da Daular Usmaniyya tuta ta hanyar wani kasaitaccen buki wanda shi ne irinsa na farko a Sakkwato wanda ya shirya ta amfani da shawarar masana tarihi domin nuna gamsuwa da Jihadin Shehu Usmanu Dan Fodiyo da ya cika shekaru 200 a lokacin. Ya gayyaci dukkanin mutanen dake da alaka da Daular Usmaniyya daga kowanne sashe na Afirka da kuma gidajen sarautar da ke rike da tutocin da da daular ta rarrabawa almajiran Dan Fodiyo da su ke cikin yankin Afrika ta Yamma domin halatar wannan muhimmin taro domin tattauna muhimman tsare tsaren daular domin a gwama su da zamani. Mabiya wasu addinai da ba na Musulunci ba, sun halarci taron domin sanin irin tanadin da daular ta yi dangane da su, domin ganin sun gudanar da addinin su cikin lumana da kwanciyar hankali.
Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido mai saukin kai ne, bashi da girman kai, yana girmama kowa yaro da babba. Yana da kyauta kwarai, hasalima abinsa na mutane ne. Yana da farin jini tamkar watan Sallah. Dukkanin yada lamura suka kasance bashi tunani ko neman taimakon kowa illa Allah, yana da wuya kasan bacin ransa da sauri. Har ya rasu yana Kiyamul Layli da Sallar Waluha tare da yawan Sallatul Ibrahimiya da uwa ba Karatun Kur’ani da Dala’illul Hairati.
Bayan kammala shagulalan Sallah Karama a shekarar 2006, Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido ya tafi Babban Birnin Tarayya watau Abuja domin halatar wani taro a kan Ilimi wadda ya gudana a karkashin Jagorancin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda daga bisani ya gana da Shugaba Obasanjo. A ranar 29 Ga Watan Oktoba na shekarar 2006 ya shiga Jirgin ADC domin dawowa Sakkwato, yana tare da dansa Sanata Badamasi Maccido da jikansa da wasu masana da suka halarci taron karawa juna sani a kan Ilimi. Jirgin ya yi hatsari mintocin kadan da tashinsa a Babban Filin Sauka da Tashin Jiragen Sama dake Abuja. Dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin suka rasa rayyukan su har da Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido. Sai dai gangar jikinsa ba ta kone ba, kamar na wasu fasinjojin da dama, an samu gawarsa yana rike da Kur’ani da Dala’illul Hairati Allahu Akbar. Dubun dubatan mutane ne suka cika garin Sakkwato domin yi masa Sallar Jana’iza daga bisani a wannan ranar aka rufe shi a Hubbaren Shehu Usmanu kusa da Mahaifinsa Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku.
Shekaru ashirin da rasuwarsa, gudumuwarsa da kyakkyawan ayyukansa har yanzu sun kasance hasken ci gaban Daular Usmaniyya da kuma kasar Nijeriya baki daya. Allah ya ambace shi cikin mazauna Jannah Firdausi tare da sauran Musulmin da suka rasu Ameen.
Alkammawa ya rubuto ne daga Kaduna Nijeriya













