Shekara 44 Na Sarkin Zazzau: Bai Gaji Da Mutane Ba, Ba A Gaji Da Shi Ba — Kabiru Kafinta

An bayyana shekara 44 da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi a karagar masarautar Zazzau da cewar, shekaru ne da babu wani Bazazzagi da zai ce mulkin Sarkin Zazzau ya dame shi, shi ma bai taba cewar al’umma sun dame shi ba.
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Alhaji Kabiru Kafinta, jigo a kungiyar ‘yan kasuwar katako na kasuwar Sabon gari, a tsokacin da ya yi kan cikar mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idrisshekara 44, a karagar Zazzaju.
Alhaji Kabiru Kafinta ya ci gaba da cewar, rayuwar mai martaba Sarkin Zazzau, rayuwa ce wadda babu wani dan asalin Masarautar Zazzau da ma jihar Kaduna da bai amfana da kyakkyawar shugabancin adalci na mai martaba Sarkin Zazzau ba.
A nan ne Alhaji Kabiru ya kuma bayar da misali da duk lokacin da mai martaba Sarkin Zazzau zai yi jawabi, babban jigon jawabinsa a kowane lokaci, shi ne batun zaman lafiya da yin kira da al’umma su rungumi addu’o’i, domin samun zaman lafiya a masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.
A dai zantawarsa da wakilinmu ya yi addu’a ta musamman ga mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, na yadda yake nuna damuwarsa a duk lokacin da aka sami matsalar gobara a kasuwar ‘yan katako, mai martaba Sarkin Zazzau da kan sa ke ziyarar kasuwar ‘yan katako domin jajentawa ‘yan katako da matsalar ta shafa.
A karshen ganawar wakilinmu da Alhaji Kabiru Kafinta, ya yi kira ga al’ummar masarautar Zazzau da su tuna lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, mai martaba Sarkin Zazzau ya jagoranci
tabbatan zaman lafiya a Yelwan Shandam ta jihar Filato, wannan ya nuna rayuwar mai martaba Sarkin Zazzau, rayuwa ce da ta zama babbar inuwar da ake kirar ta Kadaura ga al’ummmomi da dama, ba al’ummomin masarautar Zazzau kawai ba.

Exit mobile version