Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Shekara Uku Bayan Kula Da Tsaron Zabe Mafi Inganci Sulaiman Abba Ya Tsunduma Siyasa

Published

on

Shekaru uku bayan da tsohon babban sufeton ’yan sandan Najeriya, Alhaji Sulaiman Abba, ya jagoranci kula da harkokin tsaron zabe mafi inganci a tarihin Najeriya a 2015, a yanzu haka ya tsunduma cikin harkokin siyasa kai-tsaye, inda ya fara da tsaya wa takarar sanata a majalisar dokokin kasar.

Hakan ya fito fili ne lokacin da tsohon IGP din, Sulaiman Abba, ya yanki tikitin shiga takarar a ranar Litinin da ta gabata a hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja, inda ya ke neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar sanata mai wakiltar Jigawa ta Tsakiya.

Idan dai za a iya tunawa, Sulaiman Abba shi ne babban sufeton ’yan sandan Najeriya a 2015 lokacin da hukumar zabe a karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega ta gudanar da zaben da duniya ke kallo a matsayin shi ne mafi inganci a tarihin kasar kawo yanzu, wanda ya kai ga faduwar gwamnatin PDP mai mulki a lokacin karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Masu kula da al’amuran yau da kullum na kallon Abba a matsayin jigon hana aiwatar da magudin zaben da a ka shirya a wancan lokaci, inda ya yi burus da duk wata tursasawa daga gwamnati mai ci ya ki yarda da sauya sakamakon zaben ko kuma yin duk wani abu wanda zai taimaka wa gwamnatin lokacin, don ta samu zarcewa.

Daya daga cikin manyan laifukan Abba shi ne, sauye-sauyen jami’an tsaro masu kula da harkokin zabe da ya yi a daren jajiberen ranar zaben, inda a ka yi ittifakin cewa, wannan sauyin da ya yi na dare daya ya taimaka gaya wajen baddala duk wani shiri da a ka kulla na tafka magudi a zaben na 2015.

Zargin da a ke yiwa gwamnatin a wancan lokaci ya sake fitowa fili ne, inda Jonathan ya tsige Sulaiman Abba jim kadan bayan kammala zaben. Majiya mai tushe ta tabbatar wa da LEADERSHIP A YAU LAHADI cewa, ’yan jam’iyyar PDP na hannun daman Jonathan a wancan lokaci su ne su ka yiwa tsohon shugaban kasar matsin lamba a kan lallai sai ya sauke Abba, saboda asarar da ya jaza mu su, duk da cewa lokacin ritayarsa ba ta yi ba.

An ce, babban abinda ya sake dagula wa gwamnatin lokacin lissafi da bata mu su rai da ya yi shi ne, yadda ya kashe wayarsa bayan ya aike da umarnin yin sauyin wajen aikin a cikin daren, ya kuma ki yarda ya kunna har sai da gari ya waye ta yadda lokaci ya yi kurewar da PDP ba za ta iya sake daukar kowane mataki ba. Kashe wayar ya hana masu fada a ji na gwamnatin tuntubar sa, ballantana a samu hujjar cewa ya ki bin umarni ko kuma a tursasa shi ya amshi umarnin.

A yanzu fitowar Sulaiman takarar ta karfafa gwiwar cewa, mutane masu nagarta irinsa sun yarda sun fara shiga cikin harkokin siyasa kuma hakan na iya tsaftace siyasar kasar, idan a ka yi la’akari da yadda ya sadaukar da aikinsa a baya, don tabbatar da cewa an samu ingantaccen zabe a Najeriya, daidai da muradin talakan kasa.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar jim kadan bayan yankar tikitin, Abba ya ce, ya shiga harkokin siyasa ne don cigaba da bai wa kasa cikakkiyar gudunmawa mai ma’ana, don gina ta.

APC ta tsayar da ranar 27 ga Satumba, 2018, don zabem fitar da gwani na majalisar dattawa ta kasa na 2019.

“Na tsunduma cikin harkokin siyasa ne, don aniyata ta kyautata rayuwar al’ummata a majalisar dokoki ta kasa da kuma sake bada gudunamawata a mataki na kasa, wanda hakan zai samu ne ta hanyar wakiltar kananan hukumomin yankina guda bakwai da ke jihar Jigawa.

“Hakan zai kuma ba ni damar zama tare da sauran abokan aikina wajen yanke hukunce-hukuncen da su ka shafi kasata a siyasance da tattalin arziki da rayuwa, don dawo da Najeriya kan tafarki na nagari.”

A yayin da a ka tambaye shi ra’ayinsa kan kin amsa gayyatar da babban sufeton ’yan sanda na yanzu, IGP Idris, daga majalisar dattawan ta kasa, sai Abba ya ce, “tabbas idan ni ne zan ba shi shawarar ya amsa gayyatar. Ba na ganin cewa akwai mutumin da ya fi kowa dacewa da ya kare ka a ko’ina face kai kanka.

“Eh, mu na da lauyoyin da su ke iya kare mu ko wakiltar mu a kowane hali, amma a ko yauhse ka zama mai kare kanka da kanka ya fi.

“A baya Ina zuwa gaban majalisa a koyaushe ta bukace ni. Ko da a lokacin da wasu ke da wani ra’ayi na daban na rika amsa gayyatar majalisar a gaban kwamitin majalisar dattawa don gabatar da abu a fayyace.

An nada Abba a matsayin babban sufeton ’yan sandan Najeriya ne a watan Agusta na 2014. Jonathan ya sauke shi daga mukaminsa ne a watan Afrilu na 2015 jim kwanaki kadan bayan sanar da faduwar shugaban kasar a babban zaben kasar, inda a ka maye gurbinsa da Solomon Arase.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: