Ammar Muhammad" />

Shekarau Ya Lashe Kujerar Sanatan Kano Ta Tsakiya Da Gagarumin Rinjaye

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya lashe kujerar Sanata a Kano ta tsakiya.

Shekarau na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 506,276 inda ya kada abokin hammayarsa na jam’iyyar PDP Ali Madaki wanda ya samu kuri’a 29,775.

A hirarsa da BBC bayan sanar da sakamakon zaben, Shekaru ya ce babu wani sanata a Nijeriya da ya samu yawan kuri’unsa.

Ya kuma yi watsi da zargin cewa ba zai goyi bayan Buhari ba a Majalisa Dattawa, yana mai cewa mahasadda ne ke son hada shi da Buhari.

Tsohon gwamnan ya ce zai ba shugaba Buhari cikakken hadin kai musamman wajen tabbatar da sasanci tsakanin bangaren majalisa da bangaren shugaban kasa.

 

Exit mobile version